Fura

430 9 3
                                    

Kayan hadi:
Gero
Sugar
Kayan kamshi

Yanda akeyi:
A wanke gero, a tsince sannan a sirfashi.
In ya bushe  asa a turmi da kayan kamshi su citta da kanunfari a dakashi har se yayi laushi yayi lukui, za'a iya saka sugar in anga dama.
A barshi a turmi a dora ruwa, inya tafasa a dinga debowa da kadan ana zubawa a turmin ana dakawa har se ya cure ya hade jikinsa yayi danko.
Daganan se a mulmula zuwa shape din da ake so.
Fura ana siyarwa a ko ina kuma ana sha da Nono ko Kunu.
Amma idan akayi a gida, za'a ji banbanci sosai akan na siyarwa harde ba'a saka kiwa da kyashi ba wajen yi.

*******************
Vote, comment and share.
Thank you.

Special Dishes In HausaWhere stories live. Discover now