Assalamu Alaikum ❤️
Gaskiya nayi kewar rubutu, shi ma yayi kewa ta. Abu ne da ke sani nishadi duk lokacin da nake yin sa.
Nayi matukar kewarku, dafatan na same ku lafiya? Kar ku gaji da ni, goyon bayanku nake nema dari bisa dari, mu gudu tare mu tsire tare❤️
***
BABI NA DAYA
ABUJA, NIGERIA.
September,2013
Bacci take tana fitar da numfashi cikin sauri kamar wacce ta yi tseren wasan gudu. A hankali ta dunkule jikinta waje daya tamkar an yi ma ta bushara da cewa za a yanki wani sashe na jikinta.
A firgice ta tashi tare da furta "Hasbunallahu wa ni'imal wakeel". Sannan ta zauna saman gadon tare da dafe kanta dake ma ta barazanar tarwatsewa. Idan da sabo ta saba da irin wadannan mafarkan, amma har yau ta kasa sabawa da irin yanayin da ta tsinci kanta.
Sau ba adadi ta kan yi nadamar kasancewarta a doron kasa.
A hankali ta tashi ta shige bandaki don watsa ruwa ko ta ji karfin jikinta da ya yi ma ta lakwas!
***
"Safeena yan matan Mami, irin wannan kwalliya haka?"
"Uhm!".
"Ni fa matsala ta dake kenan, ba a abun arziki da ke. Miye na wani Uhmm kamar wacce a ka daure ma baki".
"Wai Ya Khalil dole ne maganar ka kyale ni mana".
Ta fadi maganar ba tare da ta kalle shi ba.
"Safeena! Ubanki nace. Yanzu yayan naki kike daga ma murya? Idan ana haihuwar kaji ai Khalil ya yi jika dake".
Ta turo baki tare da gyara mazaunin gilashin da ke idonta.
"Na tafi makaranta muna da tutorial, sai na dawo Mami".
"Ki jira Khalil ya wuce da ke mana tunda duk hanyar ku daya".
"Ni fa sauri nake Mami, wallahi bata mun lokaci Ya Khaleel zai yi".
Ta sa kai ta fita ba tare da ta jira ta ji mi Mami za ta ce ba.
"Wai Mami mike damun Safeena ne? Anya kuwa ba sai ta ga therapist ba? Ni wallahi al'amuranta kara rikitani suke yi, sam babu walwala a tattare da ita tun ina tunanin miskilanci ne irin na ta, yanzu abun ya wuce a kira shi hakan, gaskiya abun na daure mun kai Mami".
"Dan ba tare da ita ka ke zaune ba shiyasa, ni kaina abun ya isheni. Watarana ka ganta lafiya lau, har mu zauna mu yi fira sosai, idan kuwa abun na ta ya motsa yanda kasan wadda aka yi wa wahayi sai ta birkice ta koma zaman daki. Idan ka ga ta fito makaranta za ta".
"Ai kuwa ba za mu zuba ma ta ido ba, dole a san abinda ke damunta, da kyar idan ba wani disorder ke gare ta ba".
"Ni dai nayi iya kokarina sam ta ki saurarena. Nayi tambayar duniyar nan ta fada mun matsalarta ta ki ta fada. Har wajen Amminta na tura ta kila ita ta fada ma ta amma ina ita ma din babu wata nasara. Kila kai idan kayi ma ta magana ta saurare ka. Addu'a ce kullum bana gushewa daga yi ma ta ita".
"Zan kokarta in gani Mami, idan ma ta kama sai ai aje asibiti kila tafi samun sukuni ta fadi ma likita abinda ke damunta, ta yiwu shi ta fada ma sa. Kin san wasu lokuttan mutum kan ji shi a irin yanayin da zai fi samun security wajen fadawa bare matsalar shi fiye da wanda ya sani".
"Duk yanda ka yi dai-dai ne. Allah ma albarka".
"Amin Mamina ta kaina".
Ya kai ma ta sumba a kunci, ta yi murmushi tare da fadin "ba ka girma Khalilun Mami. Yanzu idan Haayaa ta ganka fa dariya za tayi ma. Daddy sukutum da guda yana shagwaba".
•••••••
Tutorial suke amma sam hankalinta baya kan abinda suke tattaunawa akai. Ta tafi wata duniyar daban.
Nauwarah ta taba kafadar ta "Toh uwar yan tunani tashi mu tafi tunda yau dai kinyi asarar wannan toturial din, dama gida kika yi zamanki da yafi".
Ta ja wani gauron numfashi ta saki.
"Gara in fito in kalli halittun Allah ko na ji dadi". Ta sabi jakarta , Nauwarah na biye da ita a baya har su ka zo bakin motar Nauwarah ta bude ta shiga.
Nauwarah ta wurgo ma ta mukullin motar tana fadin "Babe na gaji da zama direba, yarinya ja mu mu tafi yawo".
"Ai kuwa ba ki isa ba, salon in barar da mu a titi ki ke so? Idan kin gaji da rayuwar ni da saurana. Ke ni fa gida za ki maida ni ba inda zan je. In ba so ki ke Mami ta mun masifa ba".
"Miye na masifa bayan ta san duk rintsi duk wuya muna tare".
Safeenah tayi murmushi har fararen hakoranta suka fito reras! Tamkar ita ta jera su.
"Ki ce mun har gidan Iliyasu muna tare, ke uwargida ni amarya". Ta fada tana murmushi.
"Na ji dai mu tafi hakanan ni fa har yunwa ina ji".
Da haka suka fita daga cikin harabar makaranta, Nauwarah na tuka su, ba ta zarce da su ko'ina ba sai kofar gidansu.
Safeenah dake zaune ta gallara ma ta harara ba tare da tace komi ba. Duk wani annurin da ke saman fuskarta ya dauke dif! Kamar an kashe fitila.
Ba kasafai ta fiye son gardama da mutane ba, musamman ma Nauwarah da take ganin ta isa da Safeenar, saboda aminci da shakuwar da ke tsakaninsu.
"Ki yi ki gama hade fuskar kamar kashin shanu, Allah sai kin shiga gidan nan ki yi ma Hajiya bayani da kanki".
A haka su fito bayan ta yi parking motarta a harabar adana motoci ta gidan. Babban gida ne na alfarma wanda da gani babu tambaya gida ne na hamshakin mai kudi.
Safeenah ta kalli gefen hugunta tana kallon motar da ke ajiye a gefen su, tsaki tayi a fili tare da bin Nauwara da tayi hanyar da za ta sada ta da main sitting room na gidan.
Suna shiga Hajiyarsu Nauwarah ce zaune , dattijuwa mai tattare da jikin huta da ba za ka taba cewa ta cimma shekaru sittin ba.
Nauwarah ta zauna gefen Hajiya tare da kwantar da kanta saman kafadar Hajiya.
"Matsa ki ban waje, ga diyata nan yau kafadar ta ta ce". Safeenah tayi murmushi tana a zaune kasan dadduma mai taushi tana gaida Hajiya.
"Ba dan kar waccan yarinyar tayi mana dariya ba, dana ce mun yi fada Safeenah".
"Ai kun ma yi fadan kuma na gani, Allah Hajiya da kyar fa na jawo ta gidan nan".
"Matso nan ki fada mana laifin da muka yi a ka daina kawo mana ziyara, fada mun ni ko Nauwarah waya bata ma ki rai".
Ba ta san sadda hawaye suka zubo ma ta ba, ba kuma na komai ba sai dan jin dadin yadda iyalan gidan suka damu da al'amuranta. Ta ji kaunar iyalan Engr. Abubakar Isah na ratsa zuciyarta da bargon da ke cikinta. Kauna ce daga Allah wadda babu algus a cikinta.
Hajiyar ta taso har gaban Safeenah ta ce "tashi 'yata , fadi mun damuwar ki". Ta girgiza kai tare da fadin "Hajiya babu komi, ban samun lokaci ne yanzu sosai".
Hajiyar dai ta ji ta ne ba dan ta yarda da ita ba.
Duk yadda ta so ta saki jikinta a gidan sam ta kasa, ji take kamar a saman qaya take zaune. Sai gab da maghriba ta yi shirin tafiya shi ma da kyar su ka bar ta don ita Safeenah tana daga cikin jerin mutane masu shiga rai duk da rashin son mutanen ta.
"Kash na manta saqon da Hajiya ta bani in ba ki, jirani in dauko".
"Shine ba ki fada mun ba, to mu je in ma ta godiya".
Juyuwar da za ta yi kenan tayi arba da shi ya sanyo kai cikin sitting room din, sanye da riga da wando kirar Armani, sumar kanshi ta kwanta luf kamar wani bakin balarabe. Yana ta zuba kamshi da alamar masallaci zai tafi.
Tayi saurin juyawa ta fita, kafin ta sa kafa har ya iso inda take yana kallon kwayar idonta, tayi saurin sadda kanta kasa.
Bugun zuciyarta ya karu tamkar zata yi tsalle ta fado.
Don't forget to hit the Like and comment sections 🥰❤️..
Ya kuke ji game da labarin nan?
Shin minene jigon labarin a taku fahimtar?
Ina jiran amsoshin 😍
YOU ARE READING
TA WA KADDARAR KENAN!
RomanceTAWA KADDARAR KENAN! Labari ne na matashiya Safeenah Aliyu Sardauna. Akwai gwagwarmayar rayuwa tattare da labarinta. Kashi 80 na labarin ya faru a gaske. Ku biyo ni dan jin irin gwagwarmayar rayuwar Safeenah Aliyu Sardauna #1 in northernigeria on 26...
