KU DUBE MU

974 46 8
                                    

*KU DUBE MU*🤲🏽

*Batul Mamman*💖

_Shimfida_

Ruwa ne mai karfi yake sauka kamar da bakin kwarya a cikin jejin gari yayi duhu baka ganin komai sai tashin kura, hayaki da wutar da ruwan bai gama kashewa ba. A gefe guda kuma maza ne guda biyu suke gudun ceton rayukansu sakamakon bomaboman da suka tashi a wurin har uku ga harbin bindiga da bazasu iya tantance takamaimai daga ina yake fitowa ba.

A motocin yaki uku suka fito banda wata babbar range rover da suka ciko. A lissafe sun kai mutum ashirin da takwas amma su biyun suka rage. Duk inda ka juya gawarwaki ne kwance cikin ruwa da jini. Kallo daya zaka yiwa wurin zuciya ta tsinke kaji inama dai mafarki ne. Duk mai imani bazai so koda makiyinsa ya tsinci kansa a wurin ba.

Sojoji ne wanda gwamnatin tarayya ta Nigeria ta tura domin kwantar da tarzoma a kasar Liberia aka yaudaresu da false information (labarin karya) suka fado dumu-dumu cikin 'yan tada kayar baya. Sun taho da niyar taimakon mutanen wani gari da akace 'yan tada kayar bayan sun kama ashe tarko ne aka dana saboda jin haushin shigarsu fadan da ba na kasarsu ba da akeyi.

Sojoji biyun da suke gudu matasa ne da basu wuce shekaru talatin ba duka su biyun. Hankulansu a tashe kunnuwansu basa jin komai sun dode saboda karar bomb ya yi musu karfi.

Mafi tsayin cikinsu wanda da alama yafi dayan sauran kuzari ne ya hango shugabansu a wannan fitar mutumin da yake tsananin mutuntawa kwance yana daga hannu. Baya yayi da sauri dayan yayi masa kallon mamaki "kada kace min komawa zakayi? Kazo mu bar wurin nan don Allah"

Kallon abokin nasa yayi ya sake kallon Major din ya koma gareshi a guje. Dago shi yayi da zafin nama sautin harsashi yasa shi komawa ya kifa a kansa suka fadi tare. Wata siririyar kara Major din ya saki mai cike da tsananin azaba wadda ta saka shi kai duba gareshi. Wani mummunan firgici ne ya saukar masa ganin kafar Major din ta dama a gutsire bomb ya tarwatsata. Zuciyarsa ce tayi nauyi ya soma kokarin daga shi domin su gudu.

Wata damka yaji ya kai masa ruwa yana wanke musu fuskoki "Lieutenant get out of here"

Bai saurare shi ba ya ciccibe shi duk da cewa ya fishi girma sosai ya saba shi a baya. Ture shi yaji yana yi yana dan dake muryarsa "this is my final command to you. Go!"

Sojoji sun horo da tsananin biyayya ga na gaba amma wannan karon bazai bi ba. Gudu ya soma yi dashi suka nufi inda daya abokin nasa yake tsaye hannunsa na zubar jini sakamakon harbinsa da akayi suka soma yankar daji.

Cak ya tsaya dayan yana cewa "muje mana"

Gabansa ke lugude ya kalli kafarsa ya dago a razane "Karbe shi ku bar wurin nan"

Major ya dan leko da kansa "Lieutenant?"

Wata ajiyar zuciya ya sauke kafin abokin tafiyar tasu ya karbi goyon bisa umarnin aminin nasa. Matsawa yace suyi nesa dashi sannan ya dago idanunsa da suka jike da hawaye sosai. Kamar mai rada yake musu bayani.

"Bomb ne"

Su biyun duka suka kalle shi a gigice. Bai nuna damuwa ba ya cigaba da magana hawayensa suna tona asirin firgicinsa. Motsi kadan zaiyi bomb din wanda aka binne cikin kasa ya tarwatsa shi. Daya bayan daya yake kallonsu

"My friend, Major this is the end"

Abinda ya dade baiyi ba ya soma shima sai kuka duka su ukun babu mai rarrashin dan uwansa.

Kafarsa ce ta danyi rawa cikin karaji yace su bar wurin. Ba yadda suka iya dole suka bar wurin a guje zukatansu suna kuka idanu na hawaye. Basuyi nisa sosai ba suka jiyo muryarsa mai dadin sauraro idan yana yi musu limanci

"Iyalina, waye zai dubi iyalina?"

Kuka ya fashe dashi sosai a hankali ya soma karanto kalmar shahada yana ji a ransa wannan ma dama ce da Allah Ya bashi.

Sunyi gudun rabin kilometer suka ji wata gigitacciyar kara wadda tayi daidai da farkawar Retired Major Mustapha ya tashi jike sharkaf da zufa yana hailala da salati ya mika hannu ya lalubo kafar katakonsa a cikin duhun dakin.

___________

Assalam alaikum wa rahmatullah wa barakatuhu. Ina mika gaisuwa mai tarin yawa a gareku baki daya

Domin samun wannan labari wanda in sha Allah zan fara posting dinsa ranar 18/2/2019, ga account number da zaku biya.

Zaku sami labarin KU DUBE MU akan *N300* wanda zaku tura ga wannan account number din.

0020332638
MOHAMMED MUSTAPHA BELLO
GTB.

Idan kun tura sai a turo min screenshot shaidar biyan wanda zanyi amfani dashi wurin saka ku a ainihin inda zaku sami labarin.

+2348091569113

FADIMEDove le storie prendono vita. Scoprilo ora