RAYUWA.

19.3K 958 99
                         
YANAYIN MAIJIDDA...

Ta dade a tsaye a wurin tana tunanin yanda har rayuwarta ta kawo wannan gaba, na farko dai ita ba kowan kowa ba, ita 'yar talaka ce, ita ba kyaun dauke hankali gareta ba, ba kuma ilimi na fada a kara ba amma gashi a dalilinta ta hada sarkakiyar da ta rasa yanda zata yi ta warware shi.

Asali ma rayuwa tayi mata kunci tayi mata zafi, a wurin aiki ta rasa abun da yake mata dadi kowa ya juya mata baya, a gida iyayenta basu ko kula juna duk a dalilinta, sannan yanzu ga wannan!

Ita Maijidda yaya zatayi da rayuwarta ne?

Shekaru biyar da suka wuce idan akace zata tsinci kanta a halin da take ciki zata musa ko ma ta karyata, sai gashi hukunci daya da ta yanke a rayuwarta zabi guda da tayi ya dawo yana damunta, ko kadan bata danasani da zabin da tayi a wancan lokaci ko da za a MAIMAITA TARIHI hakan ne zai kasance zabinta yau ma domin kaf rayuwarta idan ta duba babu lokutan da tafi farin ciki irin shekarun nan da suka shude, haka kuma kawowan karshen su ne yasa ta rasa dukkan farin cikin ta gaba daya, duniyar ta mata zafi ta mata duhu bata da madogara.

Wani zazzafan hawaye ne ya kubce mata, nan tsakar falon Baba gwiwowinta suka sage ta zube a kasa.

Umma dake shanya a tsakar gida tana hangota ta kofar falon jikinta duk ya mace, tunani guda ne a ranta "Ya Allah ko yaushe Maijidda zata samu farin cikinta ya dawo gareta?"

FARKON LABARIN

16 SEPTEMBER 2006

Yana kallon wayar tana kara amma ya gagara dagawa, tunanin abun da zai fadawa danuwansa yakeyi, don ya san yanda sukayi dashi karo na karshe, amma ganin adadin missed calls din yasa ya daga gudun kar ya zarge shi.

"Assalamu alaikum" Abdul Ali ya fada a sanyaye.

"wa alaikumussalam warahmatullah, dole ka amsa kasa-kasa yanzu abun da kakeyi ya dace kenan?"

"Don Allah kayi hakuri bana kusa ne."

"Good, yanzu kuma abun ya kaiga ka kira sunan Allah a jumla daya da karya ko?"

Abdul Ali ya runtse idanunsa yana tunanin abun fadi duk da ya kwana da sanin cewa babu abun fadi domin karyarsa ta kare, kuma ma wa zaiyi wa karyar?

Na farko dai duk duniya bayi da kaman Dr. Rayyan hatta Hajiyarsu da ya fi kusanci da ita bta sana abubuwa game da rayuwarsa ba kaman yanda Dr. Rayyan ya sani shine abokinsa kuma danuwansa mafi kusanci wanda yafi so duk duniya, duk da kasancewar shi ya biyoshi a haife basu ko fada irin ta yaya da kanin nan, saboda irin girman da Abdul Alin yake bashi a dalilin matsayin da Rayyan yake dashi a rayuwarsa.

Kaunace tsagwaronta ta dan uwantaka a tsakaninsu, wanda ya samu asali daga dattako irin na Rayyan da kuma HALIN GIRMA da ya mallaka.

"Kayi shiru kana jina"

"OKay, yi hakuri na amince I've been avoiding you"

"Dalili?"

"Kar ka min haka Dakta ka san dalili, amma in sha ALlah ending this month ina nan tafe, amma sai ka min alkawarin kaima idan nazo bazan koma ba sai ka samu mata kayi settling"

"Sai kazo ka sama min ai."

"Ko baka fada ba, ina nan zuwa, nayi maganar ma da su Baba da Hajiya."

"Muna sa idanu don naga alama kai kam idan mukayi kuskure kayi aure ta can to sai mun biya kudi mu ganka, mutum daga zuwa karatu sai ka kama ka share wuri kayi zamanka?"

"NIma kaina bana jin dadin zaman zan taho in sha ALlah."

Nan dai 'yan uwan junan suka sallame, Abdul Ali na kashe waya ya sauke ajiyar zuciya. Dole ya tsaida shawara guda, batun aikinsa, shin yana shirye da ya koma gida yanzu ko kuwa?

KE NAKE SOWhere stories live. Discover now