GOBARA TA TASHI

15.6K 760 196
                         

Na gode da kuka zabi ku karanta labarin Rumaysah da 'yan uwanta

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Na gode da kuka zabi ku karanta labarin Rumaysah da 'yan uwanta. Wadanda suka karanta Al'amarin zuci, brace your hearts because you are in for a twist in both the characters and the plot.

Please keep the votes and comments coming. You make me happy whenever I see your comments.

Please share the story to your contacts.

love you wujiga wujiga.

And yes HALIN GIRMA WILL BE FINALLY OUT ON WEDNESDAY IN SHA ALLAH, get yours and tell me what you think about it..


Mummunar karar da ta taso daga wani sashi na gidan ne, ya yi sanadiyyar girgiza ilahirin gidan, da gudu jama'ar gidan suka firfito. Masu gadi da ma'aikatan gidan ne suka yi saurin kawo agaji, a inda aka fi tsammanin hatsaniyar ta fito.

Wuta ne ke ci, ba ji ba gani, da sauri aka fara kawo agaji, wurin ya turnike da warin hayaki da kuma na gas, wanda aka fi kyautata zaton, shi ya janyo gobarar. Motoci biyu ne suka shigo. Sannan aka yi nasarar kashe wutar da ta kama kicin din.

Hajiya Sogiji tana tsaye daga gefe tana mamakin faruwar wannan al'amarin ne, sai ta hango ta a tsaye a gefen ribibi, bala'i har diga yake yi daga fuskarta. Nan da nan ta harzuka ta isa inda take. "Atika, wane irin rashin hankali ne haka? Ashe haukar taki ta kai har za ki iya babbaka min muhalli na?"

Ga mamakin Hajiya Sogiji sai ba ta musa ba, asali ma cewa ta yi. "To sai meye? An kona din, nan ma ban bi ki cikin barci na shake ki har lahira ba?"

Hajiya Sogiji ta tabe hannunta ta-ce. "Eh, lallai na san za ki iya, ai dama dabi'ar munafuki ne ya kai maka damka ta baya ya kuma noke, baya taba fuskantarka gaba da gaba, tunda kuwa abin naki haka ne, bari yau Alhaji ya dawo, za a raba zumuncin nan, tunda baya haddasa komai, sai fitina."

"Oh! Ashe ba dadi? Duba ke fa wani bangare na dukiyar mijinki ne ya samu nakasa, shi ne za ki tada jijiyoyin wuya, ni kuma da dana yake can a kwance shame-shame. Idan kin kashe min shi fa? Sai nace me?"

Kan Hajiya Sogiji ya daure. "Kashe miki Da? Kin san me ki ke fada kuwa Atika?"

"Ko an fada miki ban san sharrin da ku ka kulla ba ke da Danki, ai ni na san da walaki, goro a miya, idan banda haka ba, ba yadda za ayi Danki ya dauki kyautar miliyoyi ya bawa jinina, ashe daman Plan dinku kenan, ya shiga motar ku hallaka shi, don kun ga shi ne Dana tilo namiji."

Hajiya Sogiji ta girgiza da furucin Hajiya Atika. "Ki kiyayi furucinki Atika. Yanzu daga yin alkhairi, sai ya koma sharri? Ta yaya Fawzaan zai cutar da Ra'id, bayan kasancewarsa jininsa?"

"Idan ba haka ba, sai ki fada min ta yadda za ayi mota sabuwa dal! tayarta za ta fashe a titi, ku dai dama kun kwance wani wurin kawai, sannan ku ka dauko ku ka ba shi. Don haka ga can tsiyarku can, wurin makanikai, idan kun tashi, ku je ku dauka, ba mu so. Munafukai kawai".

"Yanzu daman abinda yake ranki kenan, zaman da ake yi tare? Ba abin da zance miki sai Allah ya shirya, amma ana zaune, ki na irin wannan mummunar zaton, meye amfanin zaman? Ki ji tsoron Allah ki kiyayi furucinki, domin kuwa hatsarin Ra'id qaddara ce. Ki yi wa kanki fada, ki bar dabi'ar mugunta".

AMAREN BANAWhere stories live. Discover now