PART 01

21 0 0
                                    

RANAR SA'A
Ranar Sa'a

Godiya ga Allah subahanahu wa ta ala wanda shine yake da Ikon tabbatuwar komai.

Yabo Tsira da aminci su tabbata ga shugaban mu annabi Muhammad sallallahu alaihi wasallam mafakar alam.

Jinjina ga wadanda suka karfafi wannan littafi ta kowacce siga
Dr Danlami hayyo  old chairman subeb kano
Dr Nura Ali dangwauro
Mlm sale uba rimi
Mlm bala fodiyya

Fatan alkhairi  gare ku yayana
Fatima isa
Rahma isa
Abduljabbar isa
Hauwa'u isa

Allah ka jaddada Rahma ga mahaifina ka gafarta masa

Allah ya ka Kara wa mahaifiya ta lafiya da Nisan kwana

Kawar amana husaina isa

                ******
Duk da tarin gajiyar da ta d'ebo yau a makaranta hakan bai hana ta yin shirin ayyukan da take yi na yau da kullum ba, kamar yadda ta Saba ne tana dawowa daga makaranta salla kadai aka bata damar yi bayan Wannan zata shiga kitchen ne tayi musu abinci, yau ma tana dawowa abinda tayi kenan bandaki ta shiga tayi yo wanka ta dauro alwala  ta gabatar da sallar LA'asar wato salla bayan ta idar ne ta cire hijabin dake jikinta ta ajiye shi a muhallinsa sannan ta nad'e daddumar itama ta ajiye ta a gurbin ta,  ta fito daga dakin ta shigo falo  sedai yau tunda ta shigo gidan mamaki take, Saboda jin shiru yayi yawa a gidan dan haka ta fara tambayar kanta wai kodai babu kowa ne a gidan ne,  musamman ma yanzu da ta shigo falo bata ga kowa ba,  kitchen ta shiga ba tare da neman wani bahasin ina wane ina wanne ba, kitchen d'in ta shiga kamar yadda yake akan ta kullum kamar wajibine se ta dawo daga makaranta take abincin rana,  sedai yau ga mamakin ta se taga alamun anyi girkin,  ta karasa gaban kulolun da take ajiye musu abincin dan ta tabbatar wa da kan ta abinda zuciyar ta take zargi, daya daga cikin kulolun ta bude, jalof d'in shinkafa ne a ciki ,ta mayar ta rufe kular, ta karewa kitchen d'in kallo a tsanaki gani tayi komai anyi shi yadda ya dace an gyare kitchen d'in tsaf kamar yadda ta take yi idan ta gama girki, cikin mamaki take take tunanin to kodai mama ta dawo da masu aikin gidan nan ne, ta d'an jima a tsaye tana tunanin wasu abubuwa daga bisani ta fito daga kitchen d'in ta nufi dakin mamar tasu, d'alaf d'alaf ta taka matakalar benen ta tazo daidai kusa da wani kofar dakin ne ta dan tsaya ta kasa kunnen ta ko zata ji motsi, amma shiru ga dukkan alamu babu kowa a cikin dakin,  dan haka wucewa tayi ta nufi dakin mama daga kofar dakin ta tsaya ta kwankwasa kofar tare da yin sallama,
"Assalamu alaikum mama "
Sallamar ta farko a ta biyu aka amsa daga cikin dakin tare da cewa "shigo mana "
ta tura kofar dakin ta shiga kamar yadda ta Saba ta durkusa har kasa tace
"mama ina yini"
Cikin sakin fuska ta amsa mata
"lafiya lau Nasireen kin dawo "
Nasireen wani dad'i taji ya lullu6eta musamman yadda mama ta amsa mata gaisuwar ta cikin walwala babu kyara ballantana hantara,  ta dubi matar dake zaune akan gado a gabanta hannunta rike da waya tace
" mama na shiga kitchen zanyi girki kuma sena tarar da an riga anyi "
Mama tace "eh ni nasa aka yi dan kema ki huta "
Nasireen zuciyar ta bata yarda da wannan kalmar ba
Tace "mama kin dawo da masu aikin gidan ne? "
mama kan ta a sunkuye tana kallon wayar dake hannunta tace
" a a farida ce tayi "
mamaki ya sake rufe Nasireen tace "anty farida kuma yau da aikin abinci "
Mama ta ajiye wayar dake hannunta ta mayar da duban ta ga Nasireen tace
"kije ki diba ki kaiwa yayan ki kabiru yaci kema ki diba yanda zai miki ki ci "
" to mama ina anty farida naji banji motsin ta ba kuma dakin ta ma shiru " Nasireen ta fada yayin da take mik'ewa tsaye
Cikin wani irin murmushi mama tace " bata nan sun tafi unguwa ita da Kawar ta,  nima dama jira nake ki dawo unguwar zan tafi "
Nasireen ta mike tsaye zata ta fice daga dakin, mama ta Kira Sunanta
"Nasireen "
Nasireen ta waiwaya ba tare da ta amsa ba,  mama tace
" ki zuba fa ki je ki bawa yayanki yaci kinsan dai baya cin abinci a gun kowa se ke"
Nasireen tace
"to"
Sannan ta fice daga dakin kitchen d'in ta koma , ta dauko plate guda biyu ta bude flask d'in da abincin yake ciki, ta zuba abincin a plate daya ta mayar da flask d'in ta rufe, sannan ta rufe abincin dake cikin plate da daya plate ta dauko cokali, Sannan ta bude fridge ta dauko ruwa guda daya da lemo guda daya ta fito daga kitchen d'in tana isowa falo suka yi kacibis da mama tasha kwalliya ta k'yafe se kamshin turare ne ke tashi daga jikinta Nasireen ta kalli mama tsaf tace
"mama unguwar zaki tafi? "
Mama tace "Eh na tafi se na dawo "
Nasireen tace " to se kin dawo "
Mama ta wuce ta tafi, ita kuma Nasireen ta nufi dakin Yaya kabiru , se ka fito daga ainihin tankamemen falon gidan, ka zaga ya ta bayan wani corridor sannan zaka tarar da dakin, Nasireen ta tura kofar dakin ta shiga, kamar yadda mafi yawan lokuta take samun sa ya hada kai da guiwa,  yau ma hakan ta same shi tayi sallama duk da tasan baya iya magana,  ta ajiye abincin da ruwan daga gefe,  ita kuma ta zauna a kusa da shi, tace 
"sannu Yaya " ta sun ce masa daurin dake kafafun sa ta matsar da igiyar gefe,  ta bude abincin ta d'ebo a cokali ta mika masa,  amma maimakon ya karba kamar ta Saba kawai se ya kau da kan sa gefe, gefen da ya Kai kan sa nan ta zagaya ta sake mika masa,  takad'ar da abincin yayi yawa zube, bata yi kasa a guiwa ba, ta sake d'ebowa ta mika masa ya sake tankad'ar da abincin ya zube, cikin tausayawa tace "Yaya ya kake zubda abincin ne? nasan fa babu abinda ka ci, dan Allah kayi hakuri ka karba ka ci ka daina zubarwa "
ta matsa da plate d'in kusa dashi da nufin itama ta matsa kusa dashi ta lallame shi ko zai yarda ya karba yaci,  amma ina kafin tayi aune ya hankad'ar da abincin gabadaya ya zubar,  ta tsaya kawai tana kallonsa ta san dai tunda lalurar nan ta same shi babu wanda yake bashi abinci ya karba yaci sedai ita to amma kuma gashi yau ita d'in MA  yaki karba, abin ya d'aure mata Kai matuka tana tsaye akan sa idon ta duk ya ciko da kwalla zuciyar ta cike da tausayin d'anuwan nata,  yayi mata nuni izuwa ruwan robar dake ajiye a gefe,  da sauri ta dauko ruwan tana cewa "ruwa zaka sha yaya " , ta bude ruwan ta mika masa da hannun sa ya karba ya sha sosai sannan ya ajiye robar,  Nasireen tace
"to yau kuma abincin ne baka so ka ci kenan "
ta fito daga dakin  ta dawo cikin gidan ta dauki parka da tsintsiya ta je ta share dakin ta sake gyara masa, tayi mopping dakin ta fito daga dakin, maimakon ta mayar da igiyar ta d'aure shi ko ta Kira maigadi ya d'aure shi kamar yadda suke masa ina se ta manta, bata yi hakan ba ,kuma bata kulle kofar dakin ba haka ta janyo kofar ta fito ta koma kitchen ta dauki wani plate ta zubo abincin ta dawo falo ta zauna, bisa koyar war addinin musulunci idan mutum zai ci abinci ya fara da yin bismillah, hakan tayi,  tayi bismillah ta fara cin abincin Loma daya biyu daga Loma uku taji cikinta ya fara wani juyawa jin cikin tayi kamar ana yakin duniya a ciki, ta ajiye cokalin dake hannunta ta rike cikinta "Wannan Wanne irin abinci ne naci " ta tambayi kan ta sedai babu amsa,  kururuwa ta fara tana salati ta nufo waje,  hannunta rike da cikin ta,  tana tafe tana layi kamar zata fadi,  wurin megadi ta nufa
Baba megadi ganin yanayin da take ciki Shima a gigice yayo gun ta,  yana tambayar ta " lafiya me ya same ki? "
ta kasa magana se cikinta take nunawa, ganin lallai tana bukatar taimakon gaggawa baba megadi yaga bai ga ta zama ba,  ya fita waje a guje yana dube duban yadda zai samu abin Hawa, Jim kadan wani mai keke napep ya bullo tun daga nesa baba megadi ya ringa daga masa hannu alamar ya tsaya,  bayan me keke napep ya karaso baba megadi yayi masa bayani a takaice, dan haka suka ruga cikin gidan da gudu, a hakan dai suka same ta tana ta  murkususu, kinkimar ta suka yi suka saka a cikin napep d'in megadi Shima janyo kofar gidan kawai yayi, ya shiga napep suka tafi asibitu, kasancewar baba megadi yasan asibitin da ake kaiwa y'an gidan nan yayi wa mai napep d'in kwatance suka Kai ta
Emergency room aka shiga da ita basu sha wata wahala ba kasancewar sun samu Dr Ali wanda shine mamallakin asibitin kuma shine likitan gidan su Nasireen
Dr Ali yayi maigadi tambayoyi shi kuma maigadi yayi wa Dr Ali halin da Nasireen ta fito ta same shi, Dr Ali ya jinjina wa maigadi ya tambaye shi shin ya sallami me napep ne maigadi yace shi ko sisi bashi da shi da kansa Dr ya zo ya samu me napep d'in yayi masa godiya kuma ya bashi kudin sa yace ya mayar da maigadi bakin aikinsa, me napep ya dauko baba maigadi ya dawo dashi bakin aikinsa
Shi kuma Dr Ali yasa aka yi wa Nasireen duk abinda ya dace ai mata dan ceton rayuwar ta, bayan sun yi duk abinda yakamata suyi mata, binciken su ya tabbatar musu da cewa guba ta ci a cikin abinci,
Dr Ali yayi matukar mamaki da kaduwa da jin sakamakon,
dakin da aka kwantar da ita ya tsaya a kanta, hannunta drip ne a d'aure yana shiga jikinta a hankali, zuciyar sa cike da tambayoyi yake kallon ta,  sedai yanayin da take ciki koda ba barci take ba yakamata ya adana tambayoyin sa, bayan wasu dakiku da yayi yana kallon ta,  haka ya bar ta ya koma ofis din sa zuciyar sa cike da sake sake, daga karshe dai ya yanke shawarar kiran hajiya Rabi domin itace jigo ga rayuwar Nasireen, wayar hajiya RABI ta dad'e tana ringing kafin ta d'aga
bayan ta d'aga ne ya sanar da ita halin da Nasireen take ciki
Hajiya Rabi tayi matukar kaduwa da jin cewa Nasireen tana kwance a asibiti dan haka ta dubi aminiyar ta wacce ta kai wa ziyara tace "aminiya ta, akwai matsala fa "
" matsalar me kuma? "
aminiyar ta tambaye ta tana mai kallon ta
"watakila ballin mu zai tashi "
aminiyar ta ta sake duban ta cikin rashin fahimta
" ta yaya zai tashi "
"Nasireen bata mutu ba tana gadon asibiti a kwance "
"mee?"
aminiya ta tambaya cikin kaduwa da zaro idanu waje,  ita kuma hajiya Rabi ta mike tsaye cikin sanyin jiki, Sannan ta dan daddanna numbobin wayar ta Jim kadan ta kara a kunne
"hello kamal kana ina ne? "
ta tambaya daga bangaren ta tare da kallon aminiyar tata  da take kokarin mik'ewa tsaye, shi ma daga can bangaren ya amsa
"banyi nisa ba ai ina waje jen gidan da na Kai ki"
cikin sauri tace
"yauwa  yauwa maza kayi ribas ka dawo ka dauke ni an yanka ta tas"yauwa  yauwa maza kayi ribas ka dawo ka dauke ni an yanka tahi "
ba ta jira yace komai ba ta katse wayar,  zufar da take keto mata kadai ma ta isa ka fahimci  tana cikin d'imuwa se Kai wa da komawa take a falon wadda ganin hakan yasa ita kanta aminiyar ta ta shiga tashin hankali,  bayan wasu yan mintuna kamal ya shigo gidan, ganin yanayin da ya tarar da su ya fahimci ba lafiya ba,
"mama meke Faruwa ne, na gan ki haka?" kamal ya tambaye ta
"Nasireen bata mutu ba, yanzun nan Dr Ali ya bugo min waya ya sanar da ni tana asibitin sa"
"eye mama " ya fada,  ba tare da ya jira Karin bayani ba ya wuce gaba yana cewa
"zo mu tafi mama zo mu je asibitin "
Ko sallama ba su yi wa matar gidan ba suka tafi
tuki yake na gangaci son ran sa mama tace
"kai kamal kashe mu zaka yi ne? "
kamal yace " ko daya mama ina sauri ne in je in karasa aikin Da guba ta kasa yi ne"
Mama tace  "a a fa kamal wannan aikin yana bukatar nutsuwa tukunna "
"hmm" yace kawai bai sake cewa komai ba, ita ma bata sake cewa komai ba haka ya cigaba da tuki kowa yana sake saken sa a zuci, ya karyaka sitiyarin motar izuwa gida, bayan maigadi ya bude musu kofa kamal ya shigo da motar,  da sauri suka shiga cikin falon, a falo suka tarar da su farida ita da k'awayenta sun bararraje suna ta sharholiyar su,  ganin yadda su hajiya suka shigo ne yasa duk suka Mike tsaye,  kamal ya dube su a fad'a ce yace
"kin zo nan kina ta sharholiyar ki babu abinda ya dame ki"
ya dubi kawayen  nata yace
" kowacce ta Kama gabanta ku fice ku bar mana gida "
Simi simi suka wuce suka bar gidan, shi kuma kamal ya wuce ciki saman bene ya haye da sauri wani daki ya shiga , Jim kadan ya dawo gurin su hannun sa rike da wata briefcase, yana karasowa, farida ta dube shi, ta dubi hajiya Rabi tace
" mama meke faruwa ne? "
Mama tace "Nasireen ta ci abinci amma fa bata mutu ba "
Farida ta ce "to ai ni a tunani na ma bata dawo gidan taci abincin ba ma "
Hajiya Rabi tace
"ta dawo gidan kuma duk yadda muka tsara hakan aka yi "
a hasale farida tace
"wannan kwai shaidaniyar yarinya da taurin rai,  to shi kuma wancan mahaukacin fa "
Hajiya Rabi tace "ni fa ban damu da wannan ba"
kamal yace "Kun ga muje asibiti dan Allah Wannan cece kucen ba shine Mafita ba "
suka d'unguma har farida suka tafi asibiti, haka suka tafi asibiti a cikin mota ne farida ta dubi mamar ta cikin karayar zuciya tace
" mama yau da safe cikin gatse  nake cewa Nasireen ta kwantar  da hankalin ta ai yau Ranar sa, ar ta ce,  la,allah ranar sa, ar ta ta ce "
mama ta dauko hannun farida ta dora a jikin ta tace
" ki kwantar da hankalin ki,  yayan ki zai ji da komai "
da karasawar su asibitin,  kai tsaye office d'in Dr Ali suka nufa, suna karasawa daidai kofar office d'in hajiya  Rabi ta saka Kukan karya suka kwankwasa kofar, Dr Ali ya basu izinin shiga, suna shiga Dr Ali yace
" Yawwa hajiya dama yanzu nake shirin sake kiran ki, naga shiru ba ku zo ba"
Hajiya Rabi ta marairaice murya tace
" Dr ai dama lokacin da ka Kira ni na fad'a maka cewa,  dukkan mu bama gidan daga ita se d'an'uwan ta "
Dr Ali yace " to ku zauna "
Hajiya Rabi ce ta iya zama, amma shi kamal yana tsaye,  yace
" dr please sake yi mana bayanin abin da kace ya same ta"
Dr Ali ya sa hannun sa a cikin jerin fayilolin dake kan teburin dake gabansa, ya dauko wani fayil wanda ga dukkan alamu shine fayil d'in Nasireen, ya duba fayil d'in na tsawon wasu dakiku,  Sannan ya ajiye shi a gabansa ya cire glass din dake like a manne a fuskar sa tare da sauke numfashi ya dube su cikin tsanaki, yace
" maganar gaskiya kamal abinda binciken mu ya nuna shine Nasireen ta ci guba ne a cikin abinci "
Kafin su kamal suce wani abu farida ta yi saurin cewa
"ni fa duk ba wannan nake so naji ba, abin da nake son ji shine shin Nasireen tana raye ne ko ta mutu "
Hajiya Rabi ta gyada Kai tace
" uhm yauwa fa wannan fa shine abinda muke so mu ji"
Dr Ali yace
"a a kar ku damu ai an yi sa'a ma gubar da taci bata komai na cikinta ba, gaskiya yakamata ku jinjina wa maigadi, domin yayi matukar kokari sosai, dan badan yayi saurin kawo ta asibiti ba, to da yanzu wani labarin ake ba wannan ba "
Hajiya Rabi tace
" tashi muje ka kai mu wurin ta"
Dr Ali yace
" a a ba se na raka ku ba ma ku je sashen accident da taimakon gaggawa female ward room two "
a hanzarce suka tashi suka tafi inda aka yi musu kwatancen, suna tafe suna gunaguni, shi kam Dr Ali Sam bai yarda da su, dama kuma tunda yaga result wai Nasireen taci guba, gashi kuma wai babu kowa a cikin gidan, zuciyar sa ta cika da shakku da zargi, yanzu kuma da suka zo yadda ya karanci yanayin su, ya sake tabbatar masa da abin da zuciyar sa take zargi, saboda haka yace bazai raka su dakin da take ba yayi musu kwatance,  bayan kuma sun fita daga office d'in ya bi su a baya yana jin duk maganganun da suke, bayan sun shiga dakin ne shi kuma ya labe,
lokacin da su kamal suka, shiga dakin, Nasireen barci take yi sosai saboda alluran da aka zuba mata a cikin drip d'in,
Kamal ya kare mata kallo tsaf,  ya Kira Sunanta
"Nasireen! Nasireen!! "
ko motsi bata yi ba ballantana ta amsa ba,  kamal yayi k'wafa , ya dubi mamar sa yace
"mama ita barcin ta ma take hankalin ta a kwance,  matsiyaciya,  mu ta bar mu da zama da tashi "
mama tace
" ni fa hankali na ba zai ta6a kwanciya ba, muddin yarinyar nan tana raye ,dan haka kamal duk abinda ka ga ya dace kayi kawai "
tana gama fadin haka ta ruk'o hannun farida tace
"zo mu tafi "
jin haka Dr Ali yayi saurin turo kofar dakin tare da sallama
"salamu alaikum "
a kid'ime suka dube shi ba tare da sun amsa sallamar ba ,
Dr Ali ya marzaye fuskar sa kamar bai ji abin da suke fad'a ba,  kai tsaye ya karasa gaban gadon da Nasireen take kwance,  yace
" har yanzu barci take kenan bata San Ma Kun zo ba "
nan ba su ce dashi komai ba , hajiya Rabi ta kalli kamal tace
" to kamal mu dai zamu tafi gida,   ka zauna anan kayi duk abinda ya dace "
Dr Ali yace
"hajiya ya daga zuwan ku ki ce zaki tafi, ni a gani na ai ke ya dace ki zauna tare da ita "
kafin tace komai kamal ne ya matsa kusa da dr yace
" kar ka damu dr ni zan ji da komai  a gidan ma wani uzuri ne ya taso "
Dr yace
" to ai shikenan,  Allah ya bata lafiya "
hajiya Rabi ta ja hannun y'ar ta suka fice daga dakin .
bayan sun fice daga dakin ne kamal ya Kara matsawa kusa da dr yace
" Dr ina son mu yi magana dakai "
Dr Ali yace "to ina jinka fad'i abin da kake so ka fad'i"
kamal yace
" Dr ai maganar tana da muhimmanci dadai mun koma ofishin ka "
Dr Ali yace  " to  mu je office d'in ", suka fito tare , kamal yace
" bari naje cikin mota na d'auko wani sako ", dr ya bashi dama kamal ya tafi wurin da yayi Parking motar sa  shi kuma dr ya  dawo office ya zauna bayan wasu yan dakiku kamal ya dawo ofishin hannun sa rike da wata briefcase yana shigo wa ya d'ora briefcase d'in akan teburin dake gaban dr Ali ,ya ja zip d'in briefcase ya bud'e,  kud'ad'e ne a ciki rafar y'an dubu dubu a jere layi layi , ya kamal ya d'auko rafa guda biyu ya saka a gaban dr Ali tare da cewa
" wannan kudin aikin ka ne,  na ceton rayuwar Nasireen da kayi "
Sannan kamal ya mayar da briefcase ya rufe ya koma kan kujerar dake jikin teburin dr ya zauna,
dr Ali ya ciro wayar sa daga aljihun rigar sa na gaba ya ajiye ta akan teburin ya zuba wa kamal ido kawai
kamal ya jingina bayan sa a jikin kujerar yace
" maganar da nace zamu yi da kai itace inason ka k'arasa min aikin da gubar da Nasireen ta ci ta kasa yi "
Dr Ali ya dubi kamal tsaf yace
" ban gane wannan Yaren naka ba,  me kake nufi? "
kamal yayi wani guntun murmushi wanda ya tsaya iya fatar bakin sa ya sake gyara zama ya kalli dr ya kanne idon sa na  hagu,  sannan yace
" so nake ka kashe Nasireen "
ya sake tura briefcase d'in gaban dr Ali
" wannan shine kud'in aikin ka "
shi ma dr Ali jingina bayan sa yayi a jikin kujerar da yake yana kallon kamal a nazarce a cikin zuciyar sa yana tuna tsantsar rashin imani da rashin tausayi irin na wad'annan mutane,  da kuma uwa uba butulci da muguwar sakayya , wai duniya ina zaki  damu ne dr Ali ya tambayi kan sa sedai kuma maimakon ya samu amsa kamal ne ya katse masa tunanin neman amsar ta hanyar cewa
" ya kayi shiru ne a gani na aiki ne me sauki a wurin ka, kai amintaccen likitan alhaji ibrahim ne mahaifin Nasireen gashi kuma da Nasireen ta ci guba a abinci asibitin ka aka kawo ta, ko dame ka kashe ta dai result d'in bazai canja ba,  guba taci ta mutu, dan haka wannan business ne,  nasan dai yawancin ku tuni sun yi nisa da wannan kasuwancin"
dr Ali yace " nima ba rejecting abin da ka zo da shi zanyi ba, kawai dai ina tunanin lalubo hanya mafi sauk'i ne da zan aiwatar da abin da Kazo min dashi"
Kamal yayi murmushi mai cike da mugunta yace
" yauwa d'an gari ga kud'in aikin ka nan naira miliyan d'aya da rabi "
yana gama fadin haka ya mik'e tsaye tare da zura hannunsa a cikin aljihunsa
" yaushe zamu zo mu d'auki gawar,  ?" . Kamal ya fad'a cike da izgili
Shi ma dr Ali ya mik'e tsaye yana cewa
" gobe da safe "
Kamal ya mik'awa Dr Ali hannu suka misabiha tare da had'a k'irji alamar tabbatuwar kwangila.
Dr Ali ya zauna zugum ya zubawa kud'in ido a zuciyar sa yana lissafin wanne zai d'auka shin ya manta da amana da kuma amincin dake tsakanin sa da mahaifinta ne ya aiwatar ko kuma ya k'yale ta,  ko don gudun d'iban dubban zunubai.
Kamal ya fito daga ofishin likita cikin tak'ama,  gida ya koma inda ya tarar da su farida da mama,  sun kasa tsaye sun kasa zaune,  kallo d'aya zaka yi musu ka tabbatar da cewa basa cikin kwanciyar hankali,  gabad'ayansu  a d'imauce suke,  suna jin motsin shigowar kamal suka tafi wajensa kowannensu yana son jin yadda ta kaya, ganin annashuwa a fuskar sa yasa suka ji dama dama a zuciyar su, ba su ce dashi komai ba har seda suka shiga falo , cikin zak'uwa mama tace
" to kamal yaya me ake ciki yanzu? ".
Kamal yayi wata shewa har da tafa hannu,  yace
" final mama,  case closed,  tun daga yanzu ki fara k'irga awannin da suka rage zuwa safiya,  za a Kira ki, kije asibitin Dr Ali d'aukar gawar 'y'ar mijinki alhaji ibrahim gambo.
Cikin farin ciki mama tace
" da gaske kake? ".
" k'warai kuwa ".
kamal ya fad'a yayin da yake zama a d'aya daga cikin kujerun falon,  su ma zaman suka yi,  farida tace
" yaya dan Allah kayi mana bayanin abubuwan da suka faru"
Kamal yayi musu bayanin yadda suka yi da likita da kuma yadda likitan ya kar6i aikin ba tare da gardama ba. hajiya Rabi saboda farin ciki harda rangad'a gud'a kai kace rakiyar sabuwar amarya zata je
            *********************
Shi kuma kabir a lokacin da Nasireen ta fito daga d'akin sa,  ta manta bata rufe k'ofar d'akin ba, kuma bata mayar masa da d'aurin igiyar ba,  hakan yasa yayi amfani da wannan damar ya tashi ya lek'o waje bai ga kowa ba kuma babu motsin kowa,  ya koma d'akin ya bincike d'akin tsaf ko zai samu abin da zai d'auka,  duk cikin d'akin idan ba kayan sawa ba babu wani abu da ya shafe shi, dan haka a hanzarce ya fito daga d'akin,  da yazo daidai corridor da yake kusa da d'akin nasa ya shiga ciki ya la6e, Jim kad'an ya fito sad'af sad'af,  ya nufo k'ofar fita daga gidan, daidai lokacin da su baba maigadi da me napep suka cicci6i Nasireen suka fito da ita,  ganin halin da k'anwar sa kuma jininsa d'aya tilo, take ciki duk da bai san dalilin shigar ta wannan mawuyacin halin ba, yasa fashe da kuka mai ratsa zuciya, yana jin takaici da bak'in ciki akan halin da yake ciki amma bai ta6a jin irin na yau ba, ba yadda zai yi ya iya taimakon ta, yana tsaye yana kuka yana kallon su har suka tafi da ita, ko ina zasu Kai ta oho,  haka ya fito daga cikin gidan yana ra6e ra6e,  cikin sand'a ya dinga bin sawun napep d'in har ya daina ganinsa,  bayan napep d'in ya 6ace masa ne,  ya samu wani wuri ya zauna ya ci Kukan sa ya k'oshi,  bayan ya natsa ne,  ya daina Kukan ya tashi yayi gaba tafiya yake kawai bai san inda zai je ba, bayan yayi tafiya ne mai tsawo ya gaji sosai,  ya isa wani masallaci, inda ya tarar da mutane suna alwalar sallar magariba,  ya tsaya yana kallon su daga k'arshe dai ya matsa kusa da su, baya iya yin magana se nuni yayi musu a bashi buta shi ma zai yi  alwalar,  d'aya daga cikin matasan gun da suke alwalar wanda bazai d'ara kabir a shekaru ba,  ya matso kusa da kabir ya mik'a masa butar hannunsa,  cikin zancen kurame kabiru ya tambayi matashin ina ne band'aki,  kabir ya zaga makewayin yayi tsarki ya fito, abin da ya birgeshi shine,  har ya gama uzurun sa,  ya fito wannan  matashin yana tsaye yana jiransa,  kabir ya tsuguna yayi alwala ya kammala,  suka shiga cikin masallacin a tare,  ba su jima da zama ba liman ya shigo aka tada salla bayan sun idar ne, wasu sun fita harkokin su, wasu kuma suna zaune suna lazimi, wasu Karatun k'ur,ani wasu nafilfili,  shima kabiru ganin wanda suka shigo tare dashi bai fita, se ya gyara zama ya cigaba da tasbihi, har izuwa lokacin sallar isha, bayan sun idar da isshar ne wannan matashin ya nuna wa kabir shi fa zai tafi gida,  a cikin zancen kurame kabiru ya nemi da ya taimaka masa dan baisan inda zai je ba, hasali ma nan d'in bai san ko ina ne ba,  ganin yanayin da al,uma suka tsinci kansu a ciki yanzu, wato kayi wa mutum dare shi kuma yayi maka rana, tunanin hakan yasa ya d'an yi shakku akan ya taimake shi,  bayan ya jima yana nazari ne ya mik'e tsaye sannan yayi wa kabir nuni da shi ma ya taso kabiru ya mik'e tsaye Shima, wannan matashin ya nufi inda liman yake kabir yana biye dashi a baya,  su ka je gaban liman,  a tare suka durk'usa,  liman yana ganin su ya bada hankalin sa gare su, bayan sun gaisa ne malam liman ya dubi matashin nan yace
" Suleiman ya aka yi ne "?.
ance suna linzami, saurin amsawar da matashin yayi shine zai tabbatar maka da sunan sa Suleiman, Suleiman yayi gyaran murya ya sake durk'usawa cikin girmamawa yace
" malam wannan bawan Allan ne tun lokacin da zamu yi sallar magariba yazo masallacin nan, sedai baya iya yin magana amma ga dukkan alamu yana iya jin abinda aka fad'a,  to naga dare ne kuma a fahimtata yana bukatar taimako shine na kawo gun ka ".
malam liman yace
" to Suleiman duk dai yanzu ana samun matsaloli bayan ka taimaki mutum shi kuma se ya maka butulci, baza mu k'i taimakon sa ba ".
Suleiman ya sake rusunawa yace
" malam nima nayi tunanin hakan,  amma daga baya na yanke shawarar zan taimake shi "
Malam liman yace
" to ai Alhamdulillah, tunda ka yarda zaka taimake shi,  yanzu ka tafi dashi inyaso bayan ya nutsu ya huta se mu nemi sanin waye shi".
kabir da yake zaune gungurun kamar gungume ko k'wak'k'waran motsi baya yi, jin sun kammala tattaunawar shi ma ya rusuna tare da had'a tafukan hannunsa biyu alamar godiya da jin dad'i,  Suleiman ya ruk'o hannun Suleiman suka mik'e tsaye tare,  suka fito daga cikin masallacin. 'y'ar gajeruwar tafiya suka yi ba me nisa ba su ka isa wani k'ofar gida.
Suleiman ya saka hannunsa a aljihu,  ya d'auko wasu 'ya'yan mukulli,  ya bud'e d'aya daga cikin shaguna biyun dake jikin gidan, yayi wa kabir nuni da ya shiga ciki, su ka shiga cikin shagon,  matsakaici ne, kabir ya k'arewa d'akin kallo tsaf,  k'aramar katifa ce a shimfid'e , da fulo guda d'aya,  daga d'aya gefen kuma, murhun gas ne k'arami da tukunya daidai shi a Kai,  kusa da shi robobin cin abinci ne guda biyu da kofin silver babba da k'arami,  daga bayan k'yauren k'ofar kuma butoci ne guda biyu babba da k'arama se kuma jakar kaya. daga ganin d'akin dai kabir ya tabbatar cewa ana yin rayuwa daidai Misali a ciki , Suleiman yayi masa nuni izuwa katifar yace
"  zauna mana, "
Kabir ya zauna , Suleiman ya bud'e tukunyar da take kan murhun gas d'in ya zuba abinci a cikin robar yasa cokali akai,  sannan ya zubo ruwan pure water guda biyu ya kawo gaban kabir ya ajiye shi ma ya zauna yace
" bismillah mu ci abinci d'an'uwa ".
                 **********
Su kuma su kamal da mahaifiyar sa tare da farida bayan sun gama murnar labarin da kamal yazo musu da shi,
Mama tace  " ba ku ji ba fa, mu je mu duba mahaukacin can kabir, k'anwar sa ma da take da hankali taci ta galabaita,  ballantana shi,  na tabbata yanzu ya sank'ame ".
D'akin kabiru suka tafi gabad'aya kowannensu yana k'isma yadda zai tarar da gawar kabiru, a zuciyar su, daga dosar su k'ofar d'akin ne jikkunansu yayi sanyi maimakon saurin da suke suka koma tafiyar sand'a , sakamakon ganin k'ofar d'akin a wangale,  kamal ya dubi mama, mamar sa ta dube shi baki a bud'e, ba su yi wata magana ba har seda suka shiga cikin d'akin, sun duba ko ina da ina amma basu gan shi ba,  hajiya Rabi tace
" oh ni Rabi shi kuma ina shiga kenan? "
Kamal ya tsaya Jim yana tunani sannan ya girgiza kai , yace
" mama mu je wurin maigadi ya san komai tunda shine ya Kai Nasireen asibiti ".
Farida tayi saurin cewa
" ni fa dama maigadi ina da shakku akan sa ".
tun kafin su k'arasa gun sa suke k'wala masa Kira
" maigadi "!
" maigadi "!!
" maigadi "!!!
a firgici ya fito daga band'aki yana d'aure tazugen wandon sa,  yayi saurin ajiye butar dake hannunsa ya nufo gun su yana amsa kiran
" na, am hajiya,  ranki ya dad'e,  gani ".
ya durk'usa a gaban su
Kamal yace masa
" ina kabir? ".
Maigadi yace
" ranka ya dad'e yana cikin d'akin sa mana ".
Kamal ya sake cewa
" maigadi ina kabir? "
Maigadi ya sake cewa
" ranka ya dad'e yana d'akin sa mana "
Cikin k'araji da gunji kamal ya sake maimaita tambayar a karo na uku,  cikin kid'ima da gigita baba maigadi yace
" wallahi ban san inda yake ba,  ban gan shi ba ".
Su hajiya Rabi da autar ta farida suna tsaye sun yi cirko cirko
Kamal ya zaro bindiga a bayan sa, ya saita bakin bindigar a k'irjin maigadi ya sunkuyo da kan sa saitin goshin maigadi yace
" tunda naga ka fiye gardama bari na aika inda ba a dawowa kaga se ka cigaba da rik'e sirrin ka acan".
Maigadi yace
" innalillahi wa Inna ilaihi raji'un,  ban san inda yake ba, ko ita ma Nasireen d'in, dalilin da yasa na Kai ta asibiti, ita ta fito nan guna a guje tana salati tana cewa in taimaka mata zata mutu,  shine na tari mai napep ya Kai mu asibitin, wallahi bayan wannan ban san komai ba. "?
Kamal yayi ajiyar zuciya ya mayar da bindigar inda ya ciro ta, ya dubi mamar sa da k'anwar sa yace
" ina kyautata zaton lokacin da wannan rikirkitaccen tsohon zai kai ta asibiti ya bar mana gida a bud'e Wannan shi ya ba kabir damar guduwa ."
mama tace
" hakane ita ma ta k'ara matsawa kusa da maigadi tace
" sannu baba da ceton rai,  ashe har kana da basira haka?, kaga aiki a gidan nan,  tunda har zaka rik'a shiga aikin da babu ruwan ka."
ta juya ta dubi kamal tace ka ba shi kud'in sa na wannan watan ya bar min gida bana buk'atar sake ganin sa a gidan nan ".
bata jira yace komai ba tayi wucewar ta cikin gida, ita ma farida ta bi ta a baya,  baba maigadi yana ta yiwa kamal magiya yana had'a shi da Allah amma ko kad'an bai saurare shi ba  ya watsa masa kud'in,  sannan ya  tasa shi a gaba ya sa ya d'ebi kayan sa ya fice daga gidan, shi kuma kamal ya turo kofar gidan ya kulle ya dawo cikin gidan sedai bai biya ta wajen mamar tasa ba, d'akin sa kawai ya wuce ya kwanta.
Dr Ali tunda kamal ya bar asibitin sa, ya kasa zaune ya kasa tsaye, juyayin lamarin yake tare da lissafin yadda zai samu Mafita, se kaiwa yake da komowa tsakanin ofis din sa da d'akin da aka kwantar da Nasireen, yayi juyayi matuk'a,  a haka dai ya samu yayi sallar magariba da isha,  bayan idar da sallar ne yana zaune yayi jugum a masallacin dake cikin asibitin sa,  yana tunani,  can wata dabara ta fad'o a zuciyar sa,  dan haka da sauri ya tafi wurin Nasireen,  ya tarar da ita ta farfad'o , ya tsaya akanta yana kallon ta, Nasireen ta kalli dr Ali sannan ta kalli drip d'in dake d'aure a hannunta a hankali ta koma tariyar baya akan abin da ya faru da ita, Dr Ali yace
" sannu Nasireen, ya jikin naki? ".
" da sauk'i "
ta fad'a yayin da take yunk'urin tashi zaune
" yanzu ina ne yake miki ciwo ".
Dr Ali ya tambaye ta
" babu inda yake min ciwo,  kawai dai ciki na ne yake d'an murd'awa "
ta fad'a sannan ta cigaba da cewa
" Dr waye ya kawo ni nan ?".
Dr yace
" maigadin gidan ku ne ya kawo ki nan ".
tayi shiru,  shi kuma Dr Ali ya cigaba da cewa
" Nasireen a binciken da muka yi, ya nuna mana kin ci guba ne a cikin abinci, ke kuma ta yaya hakan ta faru, ko dai kin gaji da duniya ne? ".
tace  " wallahi Dr nima ban san ta yadda hakan ta faru ba."
daga nan tayi masa jawabin yadda abin ya faru har zuwa yadda suka yi da yayan ta kabir bayan ta kai k'arshe ta fashe da kuka
Dr Ali ya jinjina kai  yace
" tabbas dukkan Kuna da nisan kwana ne musamman ma ke yadda kika ci gubar, alhali guba ce mai matuk'ar hatsari saboda cikin mintuna kad'an take lalata kayan ciki, amma ke babu abin da ta lalata miki a ciki."
Nasireen ta sake fashewa da kuka, Dr Ali yace
" ai ba ki zo gun kuka ba tukunna ki bari mana,  in k'arasa miki bayani ".
Nasireen ta cigaba da Kukan ta , shi kuma yayi murmushi yace
" kamal ya bani kud'in aikin ceton ran ki naira dubu d'ari biyar,  sannan kuma ya bani naira miliyan d'aya da dubu d'ari biyar,  akan na k'arasa masa aikin da gubar da kika ci ta kasa yi."
cak Nasireen ta tsaya da kukan da take yi ta dubi Dr Ali tace
" me kake nufi kenan ?".
cikin sanyin jiki ya gyara tsayuwar Sa yace
" abin da kika ji nace".
Nasireen cikin kuka tace
" Dr ko kashe ni hakan bazai k'are ka da komai ba."
Dr Ali yace
" ki kwantar da hankalin ki Nasireen,  bazan kashe ki ba,  amma fa dole ne ki mutu koda kina raye".
" baza ka kashe ni ba amma kuma dole ne in mutu koda ina raye,  to me hakan ke nufi? ".
ta fad'a tana kallonsa hawaye yana zirnayowa daga idon ta
" Dr kashe ni dai zaka yi kenan? "
Shiru yayi bai ce komai ba, ita kuma Nasireen cikin karayar zuciya ta cigaba da cewa
" shikenan Dr ka kashe ni kawai, dan nasan ma yanzu sun riga sun kashe yayana,  wai me muka tare musu ne wad'annan mutane, me muka yi musu?  ta sake fashewa da kuka mai ratsa zuciyar duk wani mai imani
Dr Ali ya ciro wani hankici a cikin aljihunsa ya mik'a mata,  shi ma idanun sa sun cicciko da k'walla, yace
" ki daina kuka Nasireen, bazan kashe ki ba, ki sani mahaifin ki mutumin kirki ne ina mai tabbatar miki bayan sa baza ta yanke da wuri haka ba."
tayi ajiyar zuciya tace
" ban damu koda na mutu, ko ba komai zan je na tarar da Iyayena, sedai ina fargabar barin d'an uwana, Wanda ni kad'ai na rage masa"
Dr Ali yace
" ko da zaki mutu baza ki mutu a hannu na ba taimako d'aya zan miki,  amma ki jira ni ina zuwa".
ya fita daga d'akin da sauri,  daga asibitin ya fita Jim kad'an ya dawo,  ya shiga ofis d'in sa,  sannan ya dawo gurin Nasireen,  ya mik'a mata wata bak'ar leda,  Nasireen ta kar6i ledar tace
" wannan fa? ".
" doguwar riga ce a ciki, da hijabi da kud'i naira dubu d'ari biyu da hamsin a ciki, sannan akwai complementary card d'ina a ciki, ga band'aki nan ki shiga maza ki can ja kayan ki, ki fito ina jiran ki ".
Nasireen ta shiga band'aki ta cire kayan jikinta ta sake ta fito yana tsaye yana jiran ta
Ya tsaya a gabanta yace
" abin da nake nufi da kin  mutu koda kina raye shine,  ki gudu kada ki yarda su kamal sun san cewa ban kashe ki ba, saboda ban san iya tanadin da suka yi akan su kashe ku ba, idan suka san ban kashe ki ba,  ta yiwu nima su saka a kashe ni."
Nasireen tace
" Insha Allah bazan yi hakan ba "
yace " yauwa akwai kati na a cikin ledar idan kin samu  wurin da zaki zauna ko 'yan uwan ki, zaki iya tuntu6a ta"
Nasireen tace
" Nagode Dr Allah ya saka maka da alkhairi ".
ya saka ta a gaba ya rako ta har bakin get tana godiya suka rabu shi kuma ya dawo ofishin sa, wayar tangaraho dake kan teburin sa ya ta6a Sannan ya kara a kunne magana yayi a tak'aice,  ya ajiye wayar, Jim kad'an wata mace ta shigo,  cikin girmamawa tace
" yalla6ai gani "
Dr Ali yace
" Aisha samu wuri ki zauna akwai maganar da zamu yi ".
Aisha ta zauna a ladabce
Dr ya cigaba da kallonta
" Aisha duk da ba a asibiti na kika fara aiki ba, record d'in ki na rik'on gaskiya da amana ne yasa na nemi ki dawo aiki cikin wannan asibitin nawa, kuma har ga Allah a tsawon shekaru ukun da muka yi kina aiki dani ban ta6a samun wani rashin gaskiya ko cin amana a tare da ke ba".
Aisha tace
" yalla6ai wannan bada tarihin duk na menene?, ko dai nayi wani lefi ne.? "
Dr ya girgiza kai yace
" a a Aisha baki yi lefi ba, wata amana nake so mu k'ulla dake ina fatan kuma zaki rik'e min".
tace " Insha Allah,  wacce amana ce?".
Dr Ali yayi mata bayanin yadda suka yi da kamal da kuma yadda ya sa Nasireen ta gudu,  sannan ya cigaba da cewa
" inason zanyi amfani da gawar nan da aka rasa ahalinta a matsayin ita ce Nasireen,  gobe da safe misalin karfe takwas zasu zo su kar6i gawar, abinda nake so dake kada wani ko wata yasan da wannan maganar".
cikin rashin fahimta tace yalla6ai
" ta yaya hakan zai kasance, kar ka manta fa,  da kake batun wannan gawar da ta rasu aka rasa dangin ta,  police fa sun san da wannan case d'in ".
Dr yayi murmushi
" ki kwantar da hankalin ki bari nayi miki bayani yadda abin yake, na riga na sanar da DPO cewa an samu dangin wannan gawar."
cikin rashin gamsuwa tace
" yalla6ai duk da ka fini sanin aikin ka da kuma dokokin da suke tattare da case irin wannan na tsintar gawa da hanyoyin bayar da ita, ina ganin kamar hakan zai yi wuya. "
Dr yace
" babu komai Insha Allah, babu wata matsala da zata faru,  yanzu muje wajen gawar.? "
Ya fad'a tare da mik'a mata wata bak'ar leda, ta kar6a ta wuce gaba yana bin ta a baya har d'akin, suka tsaya akan gawar Aisha tace
" yau da safe kin tashi lafiya kin fito ko ina zaki je oho, aka samu wani marar imanin ya buge ki da mota, an kawo ki asibitin nan ranga ranga, amma jikin ki ko k'warzanen rauni babu, duk da k'ok'arin da mutanen dake wajen suka yi na su tsayar da direban da ya buge ki hakan bai sa ya tsaya ba, da sauran numfashi aka kawo ki nan, daga bisani kika ce ga garin ku nan. "
Dr zuciyar sa a karye yace da Aisha
" wannan tariyar bayan fa,? "
ta d'ago tare da goge k'wallar dake jikin idonta tace
" yanzu me kake so nayi"?.
" ki bud'e ledar akwai kayan Nasireen a ciki ki cire na jikin wannan gawar ki saka mata na Nasireen d'in. "
bata yi magana ba ta janyo k'arafan labulen dake gun ta saki labulayen,   suka yi musu tsakani da dr bayan ta kammala kamar yadda ya saka ta ne ta matsar da k'arafan ta fito tace
" yalla6ai na gama".
Yace " to shikenan Nagode,  Aisha yanzu ki je ki shirya se in ajiye ki a gidan ku ko.? "
tace
" to ".
ta fita daga d'akin, shi kuma dr Ali ya sa wasu daga cikin ma,aikatan asibitin su ka kai gawar , d'akin ajiye gawarwaki dake cikin asibitin.
bayan ta shirya ne ya d'auke ta har k'ofar gidan su ya kaita ya d'auki dubu d'ari ya bata da farko tak'i kar6a se da ya matsa mata sannan ta kar6a, yana daga cikin mota yana kallon ta se da taje bakin get d'in gidan su ta mik'a hannu zata bud'e k'ofar ya kira sunan ta
" Aisha ".
bata amsa ba ta juyo kawai ta Kalle shi
Yace
" ki kula da amana,  ko dan ceton rayuwar Nasireen da ta wanda ya dad'e yana dakon Soyayyar ki Dr Ali."
Aisha murmushi kawai tayi ta bud'e gida ta shiga.
**************
Ita kuwa Nasireen tunda ta fito daga asibitin gabad'aya ta rud'e,  ta rasa to yanzu ina zata je ne, ?  tsananin 6acin rai da bak'in ciki sun cika mata zuciya, ta rasa ya zata yi,  tafiya kawai take babu wurin zuwa, hawaye se kwarara suke daga idaniyarta,  bayan tayi tafiya mai nisa ne har ta fara gajiya, yasa ta yanke shawarar ta nemi abin hawa,  tunda dare ya fara, hakan kuwa tayi ta tsaya a bakin titi, har abubuwan hawa sun fara k'aranci se d'ai d'ai,  tana tsaye a bakin titi duk wanda ta tsayar baya tsayawa,  har ta fara cire tsammanin zata samu abin hawa, dan haka ta cigaba da tafiya,  can se ga wani mai keke napep,  nan ta tsayar da shi a cikin shakku,  ya tsaya ta k'araso wajensa,  ya lek'o da kansa yana daga cikin napep d'in yace
" hajiya ina zaki je ".?
Cikin muryar mai d'auke da rauni tace
" sharad'a phase two "
me napep d'in yayi Jim Sannan yace
" hajiya a wannan daren ai na zata nan kusa zaki je".
tace
" ka taimaka min dan Allah ".
Yace
" to nawa zaki bayar? ".
" ko nawa kake so,  zan baka ".
ta fad'a yayin da take yunk'urin shiga cikin napep d'in,  shi kuma ya tada  napep d'in yana tuk'in sa a tsanaki, a sannan ita kuma Nasireen gabad'aya ta koma tunanin wanda hali yaya kabir yake ciki, watak'ila ma yanzu sun riga sun kashe shi, daga sak'a haka a zuciyar ta se ta fashe da kuka, wanda har direban napep d'in yana jin sautin Kukan nata,  yaso ya tambaye ta abin da ya saka ta kuka se kuma ya ga bai kamata ya shiga abin da babu ruwan sa ba, a haka suka shigo cikin unguwar sharad'a phase two, bayan ya shigo ne ya waiwayo ya tambaye ta inda zai sauke ta, tayi masa kwatancen inda zai kai ta, bayan ya ajiye ta , ta fito daga cikin napep d'in, sannan ta bud'e ledar dake hannunta ta ciro kud'i a ciki wanda ita kanta bata san ko nawa ta ciro ba, ta mik'awa me napep, tare da cewa
" gashi Nagode "
me napep ya kar6i kud'in ya gan su da yawa yace
" hajiya wannan kud'in ai sun fi k'arfin na aiki na".
tana tafe tace
" Kaje kawai ".
ya bita da kallo cike da mamaki yace
" Nagode sosai hajiya Allah ya kawo miki mafita akan damuwar ki. " gida d'aya biyu ana uku ta tsaya a k'ofar gidan,  ta k'wank'wasa k'ofar sedai shiru ba a bud'e ba,  haka tai ta buga k'ofar amma shiru kamar babu kowa a ciki,  har ta gaji ta samu waje daga gefen k'ofar gidan ta zauna, da nufin idan ta anjima se ta sake bugawa ko zasu bud'e, haka tayi bayan ta dad'e a zaune ganin dare ya fara nisa ta tashi ta sake k'wank'wasa k'ofar amma shiru ba a bud'e mata ba, kwatakwata ma babu alamun motsin mutane a gidan, ta cire tsammanin samun masu gidan ta juya cikin takaici ta bar k'ofar gidan, a d'aya daga cikin gidajen da suke layin ne wani mutum ya  fito daga ciki, Nasireen ta k'arasa kusa da shi,  tayi masa  sallama, ya amsa sannan  ta gaishe shi nan ma ya amsa,  tace
" dan Allah malam tambaya nake".
ya dubi agogon dake hannunsa sannan ya dube ta a shak'ale yace
" yi tambayar ki, ina jinki "
ta nuna gidan da ta buga ba a bud'e ba
" masu wancan gidan nake tambaya, na dad'e ina bugawa ba a bud'e ba."
ya haska ta da fitilar waya daga saman ta har k'asa
" hala dai ke bak'uwa ce a unguwar nan"
shi ma ya tambaye ta
" eh to kusan dai hakane "
ta fad'a muryar ta a sanyaye,
" ai alhaji haruna wato mai gidan da kika nuna min, yau kwanan su uku da tashi daga unguwar nan,  ya koma gandun albasa. "
" innalillahi wa Inna ilaihi raji'un ".
ta fad'a a sanyaye,  mutumin ya kashe fitilar wayar hannunsa,  se hasken farin watan  dake sararin samaniya ne yake haska su, 
ya k'ara matsawa kusa da ita
" ko kina buk'atar taimako ne".
ya fad'a yana  yi mata wani irin kallo
" a a".
tace sannan ta fara tafiya da sauri sauri,  saboda mutumin ya fara bata tsoro,  shi kuma yayi sauri ya sha gaban ta, ta kauce ya sake shan gaban ta, 
ta kyakkya6e fuska zata yi kuka tace
" dan girman Allah kar ka cutar da ni"
" menene a hannun ki? ".
ya tambaye ta cikin barazana,  ba ta bashi amsa ba ta fara ja da baya,  shi kuma yana biyo ta, da dai ta ga da gaske zai iya  cutar da ita,  kawai se ta runtuma a guje,  ta na gudu ya na bin ta , cikin lunguna wani gun ta tsunduma k'afar ta a kwata,  wani gurin kuma ta yi tuntu6e , a haka dai har ta samu wani kango ta shiga ta 6uya a ciki , yayi dube duban sa bai gan ta ba ya hak'ura ya koma ya na k'wafar rashin nasara, ita kuma Nasareen a wannan kango ta hak'ura ta la6e saboda duk da babu agogo a hannun ta, ta tabbatar wa da kan ta yanzu dare ya fara nisa sosai,  ba za ta sake yunk'urin neman gidan wani ba kada wani abu ya sake faruwa da ita,  dan haka ta hak'ura ta samu wuri a cikin kangon ta saka ledar hannun ta a k'asa ta zauna a Kai tare da jingina bayan ta a jikin bango ta lumshe idon ta tare da tambayar kan ta
" wai yau wacce irin rana ce ne a wuri na".
wasu zafafan hawaye su ka kwaranyo kan kumatun ta ta fara tunano k'arfe shida da rabi na safiyar yau bayan ta idar da sallar asuba ta shiga d'akin matar mahaifinta wato hajiya Rabi wacce suke Kira mama, ta durk'usa ta gaishe ta,  cikin fara, a da sakin fuska ta amsa Nasareen ta tambaye ta 
" mama me za a dafa "?.

RANAR SA'AWhere stories live. Discover now