part 2

53 2 0
                                        

*M  A  R  I  Y A*
                 2023
*©️ Meemi Basheer*
               Queen
    Nagarta writers     Association N.W.A

*Bisimillahir rahmanir raheeem*

  *Chapter 2*
A frigice na shiga falo Ina haki. Allah ya so Babu kowa a tsakar gidan, mamakin abinda na gani nake faman yi, anan gidan! kwata kwata ma na kasa fahimtar mai ma gani! Ba Zan iya tantance abinda na gani ba, saide na San tabbas abin Mai Muni ne Wanda  tabbas duk Wanda za Aiwa mugun abun da abinda na gani ba k'aramin cutarsa akai ba, na cire hijab dina na chiga kitchen zuciyata na fat fat duk sai na ji tashin hankalin da nake ciki ya kau hasbunallahu kawai na shiga ja ba k'ak'k'autawa da na danji motsi sai na waiga duk na wani birkice
Girki na ji Ina son yi na Shiga dudduba kitchen d'in na bud'e store daga indomie sai lemuka sai kayan shayi, na bud'e fridge Babu komai! to me yasa ba a ajiye komai ba! Anya Zan dafa indomie a abincin dare kuwa! Bari kawai na Kira shi na ji, na fito daga kitchen d'in na d'au waya na shiga kiransa, daidai lokacin alhaji kawai na zaune gefen gado ya rafka tagumi kallo d'aya za ka yi mai ka tabbatar cewa Yana da damuwa a ransa, Yana ganin Kiran ya share sai a Karo na biyu ya d'auka.

"Ki zo Ina son ganinki yanzu" ya fad'a bai saurari me nake cewa ba ya katse. Saboda haushi sai nak'i zuwa nai zamana a falo Ina danna waya, zuciyata har zafi take alhaji lawai ya Fara saka mun ayar tambaya game da shi, me ya sa ya aureni? Ban mantawa ranar da yazo gidanmu Ana ya gobe d'aurin aure tsawa ya daka mun Wai baya son musu, amman da yake aski ya zo Gabon goshi ba Wanda yabi bayana lokacin da nace na fasa aurensa a dalilin hakan na ci d'an Karen duka wajen Inna habiba, to da na zauna nai tunani sai Naga shi Ina ga ko an b'ata masa rai ne a wani wajen. Amma abin mamaki abin na sa ma gaba yake yi.
Kiran wayarsa na sake gani har Zan share na tashi na hau sama na saka mayfi na fesa turare na fito duk da bansan ainahin sashensa ba. Amma ganin yanda sashen da ke kallon nawa sashen da takalma a bakin k'ofar na mata sai na doshi hanyar dan Ina kyautata zaton Nan ne, ilai kuwa shid'nne Yana zaune Kan kujera sai matansa biyu zaune a gefe da gefe! d'aya ta ci uwar kwalliya tana murmushi,d'ayar Kuma hijab ne a jikinsa.
Wadda taci kwlaliya cike da fara'a tace "ah! amarya sai yau za a ganki lalle munyi farin ganin", nai d'an murmushin yake na zaune a gefe.
Alhaji ya kalli su "d'azu da safe ba na ce idan akai girki a aikawa da mariya ba? Madam ya akai Haka ne?
Wadda aka Kira da madam ita ce wadda taci kwalliya tai murmshi "alhaji ai kaga jiya agabanka na aika da Mata da yake Ni ke da girki to yau Kuma Na ga umma ce da shi  ai."  Ya kai kallon ga umma " ya Haka sumayya me yasa ba aika ba?
Ta d'ago fuskarta ba yabo ba fallasa "alhaji Ni a tunanina ta yi girkinta shi yasa ban aika ba"
A zafafe ya ce " Wai me yasa summaya Baki iya dattako ba ne? kece babba Amma Sam Baki amsar girmanki yanzu me ye Haka?
"Alhaji Ni gani nake kowa ya yi girkinsa yafi."
"Ba a Nan gidan ba Babu Mai raba mini kwano agidan nan kunji dai na fad'a ba tun yau na fad'a ba." Madam Tai caraf "banda abin umma ai abin Nan ba sabo bane a wajenki, hadin Kaine idan bamu bawa mijinmu farinciki ba wa zai ba shi wannan maganar ma Bata taso ba, Ni na dauk'e Zan ringa yin abincin Ina Bata har sati dayan kafin a raba kwana."

"Ke Kika ga Zaki iya, a gaskiya madam ba na son abinda kike yi Mana a gidan Nan saboda Allah koyaushe ke sai abinda Kika zartar za a bi hakurina fa ya dad'e da k'arewa."
"Summaya bana son tashin tashina dole Abu abinda na ce, ita ba gashi da yake tana da himma da sanin yakamata ba ta amshi maganar hannu biyu."
Umma ta ja tsaki tana huci."
Madam ta ja murmushi "to Allah ya Baki hakuri."
Alhaji lawal yayi kwafa ransa yayi mugun baci. ya kalleni da nai sakatoto Ina kallonsu duk tunanina ya luka wani wajen Wai girkin gandu a iya tsarina bani da tsarin had'a girki da kishiya duk da cewa tun farkon zuwan alhaji lawal wajena ya ce mun matansa biyu da 'Ya'ya 11 sai 'ya'yan ruko samari maza 4  ta Yaya za ace Kamar ni iya da  tulun abincin Nan. Allah ya sani tun tashina nake da burin auren babban mutum ba yaro ba, tunda Allah ya had'ani da alhaji lawai  na ji sonsa ban damu dayawan 'ya'yansa ba Amma ban zaci da wani girki Haka ba." Na ja numfshi muka had'a Ido da shi yace "ke Baki magana ba" Na ga dan karna cuci kaina nace nidai bana son hadin girki Zan ringa yin nawa su suyi nasu"
"ah ji wani fallen kinibibi ke Kinga in Zaki bi abinda ya ce ki bi karki biyewa ta umma kibi abinda mijinki ya ce shine mafi aala."
Alhaji yace "magana ta Riga ta Kare ba batun tado da ita duk macen da nake aure dole tabi tsarina girki hadashi ake na gama magana, Zaki iya tafiya.

M A R I Y AWhere stories live. Discover now