Mahmood ne ya bata amsa, daman can bata sa ran samun wannan dogon bayanin daga bakin Maleek ba.

“Karya ne sun shirya hakan ne saboda su kare dansu”

Namra ta fada, a daidai lokacin da wani tunanin na dabam ya zowa yar'uwarta Nimra.

“Waye Ubansa?”

Ummi ta tambaya tana jin kamar ba zata iya kyale maganar nan hakan nan ta tafi ba. Maleek ya fara tafiya ya nufi kofar fita daga falon domin ya tsawalla dan tsayin da yayi a falon da kanennensa da kuma mahaifiyarsa.

“Sunan Yaron Ameer dan gidan Alhaji Bashir something Mr Bashir shi ma dan Kano ne”

Da wani irin karfi Ummi ta zabura sakamakon bugawar da zuciyarta ta yi cikin rashin shiri, sai ta ja numfashi da karfi. Nimra ta nufi Mahmood tana fadin.

“Ka san shi Mahmood? Kana da hotonsa?”

“Na san shi, lemme see”

Ya ciro wayarsa ya shiga Instagram yayi searching Account dinsa, a nan yayi ta haduwa da fake account da sunan nasa, sai dai be damu da hakan ba domin abun da ya kai shi Application din neman hotonsa, hotunansa ya kama ya mikawa Nimra, ita ma faduwa gabanta yayi jikinta ya fara rawa kamar marar gaskiya.

WAIRA POV.

By the time din da Eid yake tsammanin ta yi bacci sai ya kashe wutar, ita kuma ganin wutar ta mutu ya saka ta tashi zaune ta fito daga cikin dakin, a bakin kofa ta zauna tana kallon sama, taurarin da suka yi ma samaniya ido suka fara burgeta kallonsu take sosai kamin ta fara kirgasu. Tun tana zaune har abun ya kai ga ta mike tsaye ta fito waje gaba daya yana juyawa idonta na sama kamar wanda aka cewa idan kika kalli kasa zaki mutu, bata ankara ba ta ji ta bugi mutum da sauri ta dawo da dubanta gabanta sai ta yi arba da wani saurayi da be wuce sa'ar Eid ba, dariya ta yi ta sauke kai kasa tana cewa yayi hakuri, shi ma dariyar yayi ya rike walkin dake kugunsa yana kallonta.

“Ba sai kin ba ni hakuri ba, laifina ne”

“Laifina ne dai ban kalli gabana ba sai sama”

“Ba ki yi bachi ba har yanzu me kike yi?”

“Bana komai bachin ne be zo ba, kai miyasa baka yi bachi ba”

Ta tambaya yana saka yatsanta a baki tana watsa da yawun dake cikin bakinta.

“Daman na kan dade ban yi bachi ba”

“Waira....”

Kamar daga sama suka ji muryar Eid daga ita har shi juyowa suka yi suna kallon inda sautin muryar ke fitowa, Saurayin ya kalleta.

“Matsalar kenan Eid baya barin kowa ya rabe ki, ba ya barin kowa yayi magana da ke, shi yake tafiyar da ke”

Ita dai ban da kallonsa babu abun da take domin bata fahimci komai a cikin maganarsa ba, karaso Eid yayi gurin fuska babu annuri.

“Mu je ki kwanta”

“Bana jin bachi”

Ta amsa kai tsaye sannan ta juya zata cigaba da tafiya, wani irin fisgota yayi ta dawo baya da karfi ya daka mata tsawa

“Muje ki kwanta”

A ka'idarta ba a mata fada, haka zalika ba a mata tsawa, sai kawai ta fisge hannunta ta yi tafiyarta wani gefen dabam, kallon Saurayin kawai Eid yayi ya bi bayan Waira, gurin wasu manyan duwatsu ta nufa ta zauna tana kallon wajen garin iska mai dadi na kadata.

“Kar wani ya sake miki magana ki amsa?”

Ta juyo da karfi kamar ta dake shi.

“Zan amsa ko yanxu wani yayi min magana sai na amsa, ba ruwanka da ni”

WANI GARIWhere stories live. Discover now