*********

  Bangaren Kb kwa tun da ya saki Aysha sai ya ji kamar  ya yadda k'wallon mangwaro ya huta da k'uda. Dan yanzu ne yake cin karensa babu babbaka, sai ya kwana yana waya da y'an mata yara kwa ga hindu nan ita take musu komai dan ko gidan Hajiya aka kai su bata wani iya rikesu dak'er take bari su wuni, ta dai ce ya nemi mata ya yi aure dan murna fal cikinta da ya saki Aysha Daddy ne ma ya masa fushi ya kuma nuna masa bai kyauta ba. Amma abin da ya sa Daddy bai tsaurara ba sabo da yana so Kb ya gane muhimmancin Aysha ne.

  Kb sai da ya zab'a ya darje domin kuwa wata kilalliya ya samu ana kiranta Hajara bai dai yar masu kud'i bace amma kuma iya daukan wanka da kuma kyau da take dashi shi ya ja hankalin Kb ya aureta. Bayan aure ansha amarci sosai dan Kb gani yake yanzu ya yi aure, ya samu mace dede da tsarinsa sai dai me😕 ashe amarya kwata kwata bata san in da mutunci  ya dosa ba, bata ragawa Kb bare Hajiya bare kuma wata karan kad'a miya Ummulkhairi, sai ta taka har gida ta je ta yiwa Hajiya rashin mutunci kuma daga Hajiyar har Kb din babu wanda ya isa ya d'auki mataki dan gaba d'ayansu tsoronta suke. Abu d'aya ne bata yi shi ne tab'a masa y'ay'a, ba ruwanta da su Fauzy, dan tun da aka bata labarin irin  zaman da Aysha ta yi ita kuwa ta ce wallahi duk sai ta gyara  musu zama👍

  A kwana a tashi sai ga  Kb ya dawo yana da ya sanin auren Hajara,dan yanzu ta zame masa alak'ak'ai ko fita bai isa ya yi ba sai da izininta kuma ba boka ba malam kawai tsabar rashin mutunci ne. Gashi ko wane wuri zata je sai tare da Kb zasu je, sannan ya bud'e mata mota ta shiga ya bude'e mata idan zata fita🙄 Yan mata kuwa sai da ta sanya kowacce a black list ta sanya ya goge gaba d'aya numbers d'insu. Idan ya shigo gida wayarsa a hannun Hajara zata kasance bai isa ya danna waya ba kai ko kiransa aka yi sai ta fara d'auka ta tabbatar da mai kiran sannan zata bashi wayar. Gaba da gabanta aljani ya taka wuta🙃 Yanzu ne Kb ya fara ganin muhimmancin Aysha yanzu ne yake jin inama ya mai da hannun agogo baya, kai ba Kb ba hatta Hajiya yanzu tana dana sani akan abin da ta yi ta yiwa Aysha, yanzu sosai take jan jikokinta a jiki dan hajara bata  basu dad'i ba daga ita har Ummulkhairi, Daddy kad'ai take ragawa dan gaskia sosai take girmamashi, dan bata kwana uku bata je gidan Hajiya ba idan kuwa ta je bata baro gidan sai ta sanya Hajiya  damuwa,.Dan ita yanzu  Ummulkhairi  ta samu wani me mata uku zata aura sabo da ta gujewa rashin mutuncin Hajara da kuma gorin aure da take mata kuma dan Hajara ta d'aga hannu ta zabgawa Ummulkhairi  mari ba komai bane a wurinta gata da tsawo da k'iba🤣.

  BAYAN SHEKARA BIYAR

  Aysha ta samu kammala karatun ta, ta karb'i result d'inta kuma alhamdulillah  ya yi kyau sosai. Yanzu ta kara zama babbar mace ta yi k'iba abinta farinta ya dawo ha online bussiness da take yi shaddodi lesina atamfofi da sauransu, babu abinda bata siyarwa tana samun kudinta alhamdulillah  babu abin da suka nema suka rasa dan dai Daddy ma yana taimaka musu.

Yanzu kawu Habibu ne Umma ta sanya shi ya sa Aysha ta fitar da miji ta yi aure, dan dama shi ya matsawa Umma ta barta ta yi karatu dan haka yanzu kuma Aysha ta kammala kuma ga manemanta nan masu mutunci shi yasa take so ta fidda wanda take gani ya dace ta aura. Duk da yau kusan shekara biyu Kb na zuwa wurinta yana  bata hak'uri  akan ta taimaka masa ta dawo dak'inta su cigaba da rayuwa🙄😕 amma ta ce babu ita babu gidansa amma duk da haka bai daddara ba kullum  sai ya zo ko da kuwa ba zata kulashi ba. Dan wataran yana jikin motarsa zai ganta ta fito tana tare da wani wanda ya fishi komai da komai, duk da daman yanzu kud'in nashi ba kamar na da ba, dan Hajara ta gama tatik'eshi ta kuma rabu dashi👎 ba ciki ba goyo💃 ta karawa rigarta iska😄

Umma ce zaune da kawu Habibu Aysha sai kuma Daddy da shi ne sanadin  had'uwar.

"Aysha inaso ki fidda mijin aure dan ni kamar y'ar da  na  haifa haka na d'auke ki"cewar Daddy.

Sunkuyar da kai Aysha ta yi dan kunyar Daddy take ji.

"Ba magana ake miki ba"Umma ta fad'a tana hararta dan tun jiya da Daddy ya cewa Umma a waya zai zo akan maganar ta gargad'i Aysha akan ta zab'i tsohon mijinta🤨 sabo  da yanzu gaba d'aya  Kb ya canja kuma ta lura har yau yana son Aysha ga nacin zuwa da yake kullum, sannan ta san Aysha ma taa son sa kuma idan ma wani ta zab'a ba tasan wayeshi ba sai ta je gidansa dan haka ta gaya mata ta zab'i wanda ta tab'a zama dashi ko dan y'ay'anta dan halin maza sai su gwara wanda ta san halinsa, zai fi wanda bata sani ba. Ta yi hak'uri  da abin da ya mata a baya ta manta da komai.

"Ki yi  magana mana kin yiwa mutane  shiru"Kawu Habibu ya ce yana kallonta.

"Ku mata a hankali mana kun san...

"Assalamu Alaikum" sallamar da aka rangad'a ta hana Daddy k'arasa maganar, Hajiya  ce ke sallama ita da Kb amsa musu aka yi tare da basu izinin shigowa. Mamaki ne ya kama Aysha da Umma na ganin Hajiya a gidansu abin da bata tab'a yi ba. ban da Daddy da daman ya san komai ka iya faruwa tun da Hajara ta koya musu hankali. Gaisawa aka yi a inda Kb da Hajiya suja shiga baiwa Aysha hak'uri  musamman Hajiya da har da yafiya take nema a wurin Aysha. Aysha kunya ta ji anan take ta yafe musu, sannan Kb ya roketa alfarmar komawa d'akinsa har da durk'usawa da rok'onta yafe masa ta yi tare da fatan Allah yafe mana baki d'aya.

  Daddy ya ji dad'i  da Aysha ta amince zata koma, daman yafi so ta koma amma dan kar ya nuna san kai shi yasa amma babu wanda zai yarda mace mai nagarta kamar Aysha ta kufcewa ahlinsa.An maida auren Aysha da Kb akan sadaki mai tsoka, a in da Aysha ta tare a gidanta ta ci gaba da kasuwancinta ba tare da takura ba. Sosai Aysha ta ga canji daha Kb gaba d'aya  kamar  sauya mata shi akayi yake wani nan nan da ita kulawa da soyayya  ita da yaranta sai sam barka sun koma rayuwa mai tsafta a inda Kb ya sauya gaba d'aya  halayensa. Yanzu ko kule kulen matan baya yi 😄

  Ummulkhairi  har gida ta zo ta rok'i yafiyar Aysha ita kuwa ta ce dama bata rik'eta ba. Su Hafsa da Husna sunyi aure  Alhamdulillah  suna zaune da mazajensu lafiya.Lallai wani abun alkairi ne yanzu  barin Aysha gidan Kb ya zama alkairi gashi ta karo karatu  ta zama wayayya tana huld'a da wayayyo gashi ta iya kasuwanci sannan  ta dawo ta samu kwanciyar hankali daga gareshi ba takura kai har ma da mahaifiyarsa sai dai sam barka.

  BAYAN WASU SHEKARU

  Yanzu Alhamdulillah  Kb ya k'ara samun bud'i sosai dan yanzu arzik'insa ya k'ara  hab'aka gashi ya samu kwanciyara hankali  ,a yanzu y'ay'ansu biyar fauzy, Amir, Amira,  sai kuma  Atika mai sunan Umma da kuma Saleh mai sunan Abba Allah  raya ya musu albarka amin.

     Alhamdulillah  anan na kawo k'arshen littafin nan mai suna GIDAN MIJINA,  abin da na fad'a  dai dai Allah yasa ya mutane su amfana dashi wanda na yi kuskure Allah  yafe mini amin.

  Masoyana ina alfahri daku a duk in da ku ke, musamman  wanda suka jure suka tsaya tsayin daka wajen min sharshi  ina godiya marar adadi👎✊

Nagode  sosai da sosai sai kun sake ji na a wani sabon littafi na mai suna

      😄😄😄😄😄😄😄😄

GIDAN MIJINAWhere stories live. Discover now