💠💠💠💠💠
©®AS-2022.*♡CIWO A JIKIN WANI¸.•💥*
'''(Kᴡᴀʀɪ)'''
Bʏ
*HAWWA__B__KUMO.*
(Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:@REAL-SMASHER.*
*AREWABOOKS:@REALSMASHER.*'''Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ.'''
'''D̶I̶S̶C̶L̶A̶I̶M̶E̶R̶:Tʜɪs ʙᴏᴏᴋ ɪs ᴀ ᴍɪx ᴏғ ғɪᴄᴛɪᴏɴ ᴀɴᴅ ʜᴇᴛᴇʀᴏʙɪᴏɢʀᴀᴘʜʏ. ɪᴛ ʀᴇғʟᴇᴄᴛs ᴛʜᴇ ᴀᴜᴛʜᴏʀ’s ᴘʀᴇsᴇɴᴛ ʀᴇᴄᴏʟʟᴇᴄᴛɪᴏɴs ᴏғ ᴇxᴘᴇʀɪᴇɴᴄᴇs ᴏᴠᴇʀ ᴛɪᴍᴇ. sᴏᴍᴇ ɴᴀᴍᴇs ᴀɴᴅ ᴄʜᴀʀᴀᴄᴛᴇʀɪsᴛɪᴄs ʜᴀᴠᴇ ʙᴇᴇɴ ᴄʜᴀɴɢᴇᴅ,sᴏᴍᴇ ᴇᴠᴇɴᴛs ʜᴀᴠᴇ ʙᴇᴇɴ ᴄᴏᴍᴘʀᴇssᴇᴅ,ᴀɴᴅ sᴏᴍᴇ ᴅɪᴀʟᴏɢᴜᴇ ʜᴀs ʙᴇᴇɴ ʀᴇᴄʀᴇᴀᴛᴇᴅ. I ʜᴏᴘᴇ ᴜ ᴡɪʟʟ ʟɪᴋᴇ ᴛʜᴇ sᴛᴏʀʏ ᴛʜᴇ ᴡᴀʏ ɪᴛ ᴄᴏᴍᴇs ᴛᴏ ᴜ.'''
'''W̶A̶R̶N̶I̶N̶G̶⚠: Tʜɪs ʙᴏᴏᴋ ᴡɪʟʟ ʜᴀᴠᴇ ᴍᴀᴛᴜʀᴇ ᴄᴏɴᴛᴇɴᴛ ᴀɴᴅ sᴛʀᴏɴɢ ʟᴀɴɢᴜᴀɢᴇ,ɪ'ʟʟ ᴡᴀʀɴ ᴜ ɪғ ᴜ'ʀᴇ ᴀᴛ ᴀ ʏᴏᴜɴɢ ᴀɢᴇ,ɪ ᴡᴏɴ'ᴛ ʙᴇ ʀᴇsᴘᴏɴsɪʙʟᴇ..'''
'''Iɴ ᴅᴇᴅɪᴄᴀᴛɪᴏɴ ᴛᴏ ᴍʏ ʟᴀᴛᴇ ғᴀᴛʜᴇʀ Aʟʜ Mᴜʜᴀᴍᴍᴀᴅ Bᴀʙᴀ Usᴍᴀɴ (B–KUMO). Yᴀ ᴀʟʟᴀʜ ғᴏʀɢɪᴠᴇ ᴍʏ ғᴀᴛʜᴇʀ ᴀɴᴅ ᴇʟᴇᴠᴀᴛᴇ ʜɪs sᴛᴀᴛɪᴏɴ ᴀᴍᴏɴɢ ᴛʜᴏsᴇ ᴡʜᴏ ᴀʀᴇ ɢᴜɪᴅᴇᴅ,sᴇɴᴅ ʜɪᴍ ᴀʟᴏɴɢ ᴛʜᴇ ᴘᴀᴛʜ ᴏғ ᴛʜᴏsᴇ ᴡʜᴏ ᴄᴀᴍᴇ ʙᴇғᴏʀᴇ,ᴀɴᴅ ғᴏʀɢɪᴠᴇ ᴜs ᴀɴᴅ ʜɪᴍ,ᴏ ʟᴏʀᴅ ᴏғ ᴛʜᴇ ᴡᴏʀʟᴅs! Eɴʟᴀʀɢᴇ ғᴏʀ ʜɪᴍ ʜɪs ɢʀᴀᴠᴇ ᴀɴᴅ sʜᴇᴅ ʟɪɢʜᴛ ᴜᴘᴏɴ ʜɪᴍ ɪɴ ɪᴛ.. Aɴᴅ ᴍᴀʏ ʜɪᴍ ʙᴇ ᴀᴍᴏɴɢ ᴛʜᴇ ᴍᴇɴs ᴏғ ᴊᴀɴɴᴀᴛᴜʟ-ғɪʀᴅᴀᴜs,ᴛʜᴇ ᴍᴏsᴛ ʙᴇᴀᴜᴛɪғᴜʟ ᴘᴀʀᴀᴅɪsᴇ.. ᴀᴍᴇᴇɴ.🤲'''
••••••••••••••01
#Tushe
'''YERWA,DANBOA LGA..'''
*BORNO STATE*
•••Gida ne babba,traditional building mai ɗauke da babban zaure sai filin tsakar gida dake baibaye da ɗakuna birjik kamar gidan haya,shigowar kyakkyawan farin dattijon mai cikar kamala da ba zai wuce 84yrs ba yasa tarin ƴan mata da samarin da suke zazzaune tsakar gidan ana cacar baki da hayaniya bazama kowa ya fara ƙoƙarin yin ta kansa,a tsakar gidan ya tsaya daga inda yake bayan ya ƙarewa ko ina kallo ya girgiza kai sannan ya fara ƙwala kiran *"FANDI!"* Kwance take bacci har ya fara ɗaukarta,duk da ba da niyyar jimawa suka zo ba ta jiyo kiran da mahaifinta yake mata,a ɗan razane gabanta na faɗuwa ta buɗe ido ta waigo tana kallon ƙofa,da sanyayyar muryarta mara hayaniya sanda yake sake danno mata kira tace "na'am Baba ina fitowa ne ɗankwali nake nema" juyo da kansa yayi ya zubowa ƙofar ɗakin kallo,a hankali ta ɗaga yalolon labulen ɗakin mara nauyi ta sako kyakykyawar farar ƙafarta waje,tunda ta shigo gidan bayan sun gaisa da mahaifin nata a ƙofar gida tabi ɗaki² ta gaisa da matan gidan,kasancewar Allah ya yiwa mahaifiyarta rasuwa shekaru da dama ta wuce can ta shiga ɗakinsu tun zamanin tana ƴan mata,da sauri ta zuro sauran jikita ta fito,kyakkyawar mace ce fara ta gaban kwatance,kallo ɗaya za kai mata kayi zaton ta haɗa jini da larabawa hancinta da huji,ko da yake asalinta ta fito ne daga ƙabilar Kanuri gaba da baya,wanda suke zaune Maiduguri a wani gari da ake kira Yerwa dake cikin Damboa local government. Kanuri suna ne na wata ƙabila daga cikin manyan ƙabilun Arewacin Najeriya,waɗanda suka taɓa kafa ɗaya daga cikin dauloli guda biyu mafiya girma a duk faɗin Afirka ta yau. Mutane ne da suka samo asali daga Yemen suna da matuƙar riƙo da al’adunsu na gargajiya,addini,karɓar baƙi da kuma uwa-uba hidimtawa Alƙur’ani da masu hulɗa da shi da suka shafi koyo,koyarwa,hadda,rubutawa da kuma masu karanta shi. Babban garinsu wato Maiduguri,ana yi masa kallon matsugunni ko kuma masaukin mahaddata da kuma makaranta Alƙur’ani,akwai wata kalma ko kuma lambar girmamawa da suke baiwa duk mutumin da ya ƙware matuƙa gaya wajen karanta Alƙur’ani (Goni) wanda da Hausa ake cewa Gwani. Daga cikin kyawawan al’adun Kanurai ababen ambato akwai girmama na gaba,zaman lafiya da kuma haƙuri da juna wanda ya janyo ake yiwa garin lakabi da Cibiyar Zaman Lafiya (wato Home of Peace) a Turance,wadda take ita ce babbar Jahar Kanurai. Manufar wannan rubutu da ka ke karantawa itace yin bayani bakin gwargwado game da suna,asali,da kuma wasu daga cikin kyawawan halayen mutanen da suke kiran kansu da suna Kanuri,bahaushe kuma yake kiransu da sunan Barebari. "Sunan Kanuri haɗaɗɗe ne daga wasu kalmomin Kanuri guda biyu KA wadda ke da ma’ana ta sanda,da kuma NURI ma’anar haske,wadda ita kuma tushenta shi ne Larabci Nur" waɗannan kalmomi KA da NURI su aka haɗa suka zama Kanuri. Dalilin samuwar wannan suna Kanuri,kamar yadda ya bayyana a tarihi shi ne cewa a farkon lamari su Kanurai sun kasance mutane ne makiyaya masu riƙe da sanda,sannan kuma fuskarsu tana haske. Saboda haka a ƙoƙarinsu na bambance su daga cikin sauran ƙabilun gurin da suke suma makiyayan ne,sai wata ƙabila mai suna Sau suka riƙa kiransu da wannan suna Kanuri. Wato kenan idan abun mu kwatanta ne sai mu iya cewa,mutane masu kama da haske waɗanda suke riƙe da sanda. Amma a wani faɗin kuma asalin sunan Kanuri gauraye ne na kalmomin Larabci guda biyu KAL da kuma NUR waɗanda idan aka haɗesu suke zama KAN-NURI a bisa ƙa’idar Larabci,waɗanda kuma za a iya fassarasu da kamar haske,kamar yadda muka ji daga kakaninmu,daga baya kuma aka jirkita su suka koma Kanuri. Kenan idan muka yiwa wannan suna fassara ta kwatance sai mu ce,mutane masu kama da haske,hakan ya nuna cewa akwai kusanci a tsakanin waɗannan maganganu guda biyu,sai dai Hausawa da kuma Yarabawa amma na iIlori kawai,suna kiransu da sunaye Barebari da kuma Baruba. Abunda za'a iya danganta shi da sunan da Sarkin Musulmi Muhammadu Ballo (1974) ya kira su da shi:"Waɗannan Barbar ɗin,ragowar Barbar ɗin da suka rayu ne a tsakankanin ƙasashen Arewacin Afirka da kuma Habasha.." Wannan shi ne sunan da Bahaushe ya jirkita shi zuwa Barebari,shi kuma Bayaraben iIlori yace Baruba. Wannan kuma saboda kusancinsu duka biyun ne da Sarkin Musulmi Muhammadu Ballo,albarkacin Jahadin Shehu Ɗanfodiyo wanda Hausawa da Yarabawan duk abu ya shafesu. Wannan suna na Kanuri shi ne sunan da ƙabilu da yawa suke kiran su da shi,musamman ma Sau,Larabawa,Kotoko,Sudaniyawa,Turawa,Itofiyawa,Turkawa,Mandarawa,Marghi,Babur,Karekare,Ngizem da sauransu,haka nan kuma ana kiran su da wasu sunayen mabambanta,yayin da wasu Ƙabilun Chadi da Sudan da suka haɗa da Najdi,Baggara da kuma Hejazi suke kiransu da suna Barnowaji,Fulani kuma suna kiran su da Kolejo. Asali Magana mafi shahara itace cewa,Kanurai mutanen Yemen ne,sun zo ne daga Zirin Yankin Larabawa (Arabian Peninsula) sannan suka zauna a wani guri mai tazarar kusan kilomita 640 daga arewacin Tafkin Chadi wanda daga baya ya zama ƙasaitacciyar daular Kanem-Bornu. Sannan kuma Sarkin Musulmi Muhammad Ballo (1974) ya ce:"Waɗannan Barebarin,ragowar Barebarin da suka rayu ne a tsakankanin ƙasashen Arewacin Afirka da kuma Habasha,su ne waɗanda Humayyar (Sunan ƙabila ne) suka kora daga Yemen.." Wanda kuma a ƙarshen bayanin nasa ya ƙare da cewa:"Sannan suka gangaro Kanem,suka zaune ta.. Asalinsu daga Yemen ne,sun taho tare da ƴan’uwansu Kanurai suka rabu da su a Ngazargamau" Yaren Kanuri kala ɗaya ne tal! Amma sannu a hankali sakamakon yanayin siyasar rayuwa da ta haddasa gaurayuwar Kanurai da wasu baƙin yarurrukan kodai ta hanyar zuwansu garuruwan Kanurai ko kuma zuwan Kanurai wasu garuruwan ya haifar da hayayyafar wannan yare inda har takai ga an samu bambamce-bambamcen wasu kalmomi ko kuma ma canjin yaren kaco-kam,daga cikin rabe-raben Kanuri akwai:Wuje,Gumati,Manga,Bodoi,Kanembu,Morr,Kwayam,Suwurti,Buduma da sauransu. 100% ɗin Kanurai Musulmi ne waɗanda suka riƙi addinin Musulunci a matsayin tafarkin rayuwarsu sannan kuma Annabi Muhammadu samfurinsu.." Gudunmawar Kanurai wajen yaɗa addinin Musulunci Gazali (2014) ya bayyana Kanurai a matsayin mutanen da suka bayar da gagarumar gudunmawa wajen yaɗa ilimin addinin Musulunci da harkar malunta a Afirka ta Yamma a matakin farko da kuma dukkan faɗin Afirka baki ɗaya. Sarkin Musulmi Muhammad Ballo (1974) ya siffanta su a matsayin mutanen da Musulunci ya yi matuƙar yaɗuwa a duk faɗin daularsu a tsakankani sarakunansu da waziransu da sauran jama’arsu,har ta kai ga yana faɗin cewa:"Kai! Ba za ka taɓa samun jama'a a cikin waɗannan garuruwan ba face sun himmatu da karatun Alƙur’ani da tajawidinsa (Hukunce-hukuncen karatun Alƙur’ani),haddace shi da kuma rubuta shi. Kanurai suna da tsagar gado a fuskarsu,wannan tsaga ta su kuwa guda tara ce da suke yin ɗaya a tsakiyar goshi wadda take farawa daga farkon goshi ta sama har zuwa ƙarshen ƙasan doron hanci,sai guda biyu-biyu a kan kumatu,da kuma ƙarin wasu guda biyu-biyu a ɓarin dama da hagu na fuska,sannan kuma dukkan tsagogin nasu dogaye ne (kalli fuskar marigayi Janar Abacha a matsayin misali..) Turus ta tsaya ganin yayyunta maza da ƙanne da suke ƴan maza zar dukansu kowanne ya watse a gurin,kamar ba yanzun nan ta shiga ta barsu ba,gidan da ke cike da hayaniya kamar suna rigima,shi ne cikin ɗan lokaci har kowa ya kama gabansa daga shigowar Baba,a hankali ta ƙarasa gaban mahaifin nata,durƙusawa tayi kanta ƙasa tace "ga ni Baba" ɗan girgiza kai Baba yayi yace "kiyi haƙuri Fandi.. Duk da na san ke me haƙuri ce,amma a wannan karon ina maki nasiha da ki ƙara akan wanda kike da shi,zama ku biyu a gurin miji sai kin koyi yanda za ki kai zuciyarki nesa.." Daga nan ƴar nasiha yayi mata mai shiga jiki sannan yace "tashi kije *ZANNAH* na jiranki za ku tafi.. Allah ya saɓa hali,ya baku zaman lafiya" gyaɗa kai tayi jikinta a sanyaye tana share hawaye tace "ameen Baba,na gode Allah ya saka da alkhairi" fuskarta sam bai nuna fara'a ba sai dai zallar biyayya,ta shiga ɗaki ta ɗauko hijabinta,dama ya faɗa mata baza su jima ba ko sunje gidan,sai dai batai zaton ƙararta zai kawo gurin mahaifin nata ba,sanda ta fito sai da tabi ɗakunan matan ƙannen mahaifinta tayi masu sallama sannan ta kama hanyar fita gidan,a ƙatuwar rumfar dake ƙofar gidan wanda Baba suke zaman hira ta tarar da maihaifin nata zaune yana sake yiwa Zannah da kansa ke ƙasa nasihar ya kasance mai adalci tsakanin matansa,shi kuma yana gyaɗa masa kai yace "in sha Allah.. Na gode Baba" yara biyu maza kyawawa zaune kusa da shi,kana kallonsu ka san duk inda suka fito jini ɗaya suke,suna ta wasansu bakinsu da alawa mai tsinke da Baba ya basu,babban duka bazai wuce shekaru 7 ba,sai ƙaramin mai 4 yrs,ganin fitowarta yasa yaran tashi,ƙaramin ciki ya rugo da gudu yana cewa "Maama yau ban yi wasan ƙasa ba,Yaa Abbor ne yake yi" wansa da ya kira da Abbor yace "Maama banyi ba,ƙarya Sanda yake yi" da kallo tabi yaranta da suke tsananin kama da juna wasu irin hawaye suna kawowa idonta,tai saurin wucewa bata kulasu ba tana share fuskarta kada yaran su gani,ta buɗe motar dake ƙofar gidan ƙirar Peugeot ash colour,sallama da Baba Zannah yayi ya taso ya kama hannun yaransa yace "baku yiwa Kaka sallama ba" suka juya sukace "sai anjima Baba" while shi kuma yana cewa "mun barku lafiya Baba" dattijon kakan nasu ya ɗaga masu hannu yace "tou Allah ya kaimu,Allah ya tsare,ayi ta haƙuri da juna.." Zannah yace "in sha Allah,mun gode sosai Baba.." Tunda ya shiga mota bayan ya buɗewa yaran back seat yake kallon yanda ta rufe fuska da hijab tana kuka,kasa ce mata komai yayi har suka bar ƙofar gidan nasu,sanda suka iso line gidansu duk a cikin Yerwa yayi parking ƙofar wani ɗan madaidaicin gida mai kyau ya kashe motar sannan ya sauka,yaran ya buɗewa duka suka sauka,ya rufe motar lokacin da Fandi ta buɗe itama ta sauka,kana kallon fuskarta za ka san ta ci kuka,abunka da farar mace fuskarta har tai jaa,shi ya buɗe masu gidan suna gaba tare da yaran tana bayansu,tsakar gida ne wadatacce dake malale da siminti sai ƙatuwar bishiyar Umbrella a tsakiya da ya bawa gidan inuwa,kana kallon gidan da iyalin gidan za ka san mai gidan Allah ya yi masa rufin asiri dai² nasa,ɗaki Fandi ta wuce ta bar yaran tare da Babansu suna ta masa hira yana biye masu,da ya gaji da saurarensu yace "maza kuje kuyi wasanku banda faɗa bari naje gurin Maama" suka ce "tou Baaba" ya tashi ya barsu a tsakar gidan,ɗakin da ta shiga ya ɗaga labule da sallama a bakinsa ya shigo,wani mad ƙamshi ya daki hancinsa ya lumshe idanunsa,tana jinsa amma bata iya ɗagowa ta kalleshi ba,ya ƙarasa bakin gadon da take kwance ya zauna,gaba ɗaya ya rasa me zaice dan har yanzu kuka take,cikin wani irin sanyin da jikinsa yayi yace "Fandi! Tashi ki saurareni magana nake so muyi" bata ɗago ba tana share hawayenta tace "ka faɗi duk abunda ya kawoka ina saurarenka" yace "kukan nan fa da kike ba zai mana maganin komai ba,sannan ba shi zaisa na fasa auren nan ba" tashi tayi ta zauna tana kallonsa hawaye suna ci gaba da sauka fuskarta tace "ƙwarai na san kukana bazai hanaka ƙara aure ba,dan Allah tunda kaima ka faɗa da bakinka ka rabu dani naji da abu ɗaya" kallonta yake babu ko ƙiftawa yace "yanzu kin fi so muyi ta zama cikin wannan yanayin? Na kula tunda na sanar maki maganar ƙarin aurena kika daina walwala.. Wanda a da ba haka muke zaune ba,ko so kike sai yaranmu sun fahimci halin da muke ciki? Dan Allah ki kwantar da hankalinki Fandi,idan baki kwantar da hankali ba ni ya kike so nayi? Sannan ita da za ta shigo duk fa da yanda kika karɓeta da haka za ku zauna,ni kuma abunda ba na so kenan,ina so ku zauna lafiya da juna,ta yanda kan ƴaƴanmu zai zama a haɗe.." Gyaɗa kai tayi tana share wasu hawaye masu zafi da suka zubo idonta tace "shi kenan.. Allah ya baku zaman lafiya" yace "ke banda ke?" Ta masa wani kallo bata ce komai ba,ya kwantar da kai yace "dan Allah ki kwantar da hankali ta haka kawai zan samu damar sauke nauyinku duka" ita dai bata ce komai ba kallonsa kawai tace,yace "ki ce wai abu uwar gidana,kuma uwar ƴaƴana" tace "babu abunda zance ka sani,aurene ka ce sai ka yi,shi kenan Allah ya baku zaman lafiya" ganin duk ta inda ya biyo ta ƙi sauka dole ya haƙura,kiran sallar asr yasa shi tashi yace "bari naje masallaci na ji ana kiran sallah" bata kalleshi ba tace "a dawo lafiya" har zai fita yace "kiyi haƙuri Fandi.." Ta ɗago a wani irin fusace dan haushi tace "wai idan ban yi haƙuri ba ya zanyi tou? Ka ce baza ka fasa aure ba,shi kenan ta shigo mana ba dai kai bane ai baza'a rabaka biyu ba dai kou?" Yanda take magana cike da kishi yasa shi girgiza kai ya fita,yaran yasa sukai alwala sannan suka fita masallaci,kafin su dawo ta tashi tayi alwala tai sallah,after tayi addu'o'inta sannan ta fita ta share tsakar gidan ta sake gyarawa ta turare gidan ko ina ya ɗauki ƙamshi,ganin har about 5pm basu shigo ba,ta shiga kitchen ɗaura masu abincin dare. Kou da suka shigo gidan wajen ƙarfe 6 ne saura na yamma,a lokacin ta kusa gama girki,Zannah ya sha mamakin yanda yaga ta kula da gidan har ta shiga kitchen,kou da yake Fandi ba daga nan ba indai wajen kula da gida ne,akwai ta da tsafta sosai ko ina yai fess sai ƙamshi yake mai kwantar da rai,fuskarta ce kawai da take babu fara'a ya dakushe shi daga yawan magana,tai masa sannu da zuwa ganin da ledoji a hannunsa ta ƙaraso inda yake ta durƙusa ta karɓa ta wuce kitchen,sanda ta ajiye ta fito ta ɗauko masu babban tabarma ta shimfiɗa,ta kawo masa ruwa,lokacin yake sanar mata "kin duba kin cire naman dake ciki?" Ta girgiza kai tana miƙewa tace "a'a" daga haka ta tafi kitchen ya bita da kallo cike da so da kulawa,sannan ya taso ya biyo bayanta,tana ta aikinta bata ɗaga kai ta kalleshi ba tace "akwai abunda kake so ne?" Yace "a'a zuwa nayi dai na rage maki wani abun" ta girgiza kai wasu hawaye suna kawowa idonta tace "a'a na kusa gamawa,kaje yanzu zan fito" kallonta ya dunga yi yanda ta juya masa baya,daga muryarta ya fahimci kuka take da shirin yi,bayanta ya ƙaraso ya rungumeta cike da rarrashi yace "me yasa kike son hana ni kusantar inda kike,bayan mun saba aiki tare?" Iya yinta tayi wajen danne kukanta,a hankali yace "dan Allah ba don ni ba kiyi haƙuri Fandi,duk abunda kika ga ya samu bawa akwai manufar faruwarsa" juyowa tayi ta shige jikinsa tana fashewa da kuka,gaba ɗaya hankalinsa ya tashi,duk yanda zai ya rarrasheta sai da yayi,kafin ya samu tai shiru,suka ƙarasa aikin tare kamar yanda suka saba tun aurensu kafin su haifi yaransu,sanda suka fito yana ta janta da hira,tun bata tankasa har ta fara,after sunje sallar maghreeb suna dawowa ta kawo masu abinci,tare suka ci da yaran,bayan sun gama sukai ta hira har aka kira ishaa. Da dare sanda suke kwance bayan sun kwantar da yaran ɗakinsu yaga ta koma can edge of the bed,haƙuri ya fara bata tai murmushi kawai underneath kishi ke cinta tana jin wani irin yanayi yana saukar mata,tunda ya fara maganar auren nan ta daina cikakken bacci,nutsuwa kuwa idan tace tana da ita tou ta yi ƙarya,sam hankalinta yaƙi kwanciya da maganar aurensa,kawai dai tana ƙoƙarin dannewa ne kamar yanda Baba yayi mata nasiha,amma ta wani ɓangaren tana mamakin dalili da abunda ta ragesa da shi,wai daga zuwa bikin aboki shi kenan mutum ya dawo mata a firgice shi aure yake so,ta kasa gane me yake faruwa da shi,lumshe idanunta tayi jinsa a kusa da ita a hankali har bacci ya fara ɗaukanta. A haka kwanaki suka ci gaba da tafiya ta ɓangaren zamansu da Zannah tana ta ƙoƙarin ɓoye damuwarta ganin yanda duk ya damu,while a gefensa shi kuma ganin yanda ta kwantar da hankalinta hakan yai masa daɗi sosai,sanda ya kawo mata kayan faɗan kishiya tai murmushi tana ta danne kukan dake son ƙwace mata tai masa godiya,ya yiwa yaransu ma ɗinkuna sosai kamar lokacin sallah,sosai cikin lokacin yai masu hidima,ya canza mata kayan ɗaki,aka sake gyara gidan,kana gani kasan amarya tana hanyar shigowa ne,sati biyu tsakani aka ɗaura auren Zannah da amaryarsa Ruqayya da ya auro daga garin Sokoto,tunda aka fara bikin kullum ne sai Fandi tai kuka saboda damuwa,ga wani irin fargaba dake damunta,wanda yasa tai rama fiye da zato,ranan da amarya za ta tare few daga cikin ƴan Sokoto manyan mata suka zo jere kafin a taho da amarya,tunda Zannah ya shigo lokacin Fandi tana tsakiyar ƴan uwanta ya sanar mata amarya da danginta suna hanya,yanda yake rawar jiki ranan tun bayan da aka ɗaura auren gaba ɗaya taji ta sare,shiga ɗaya fita ɗaya zaiwa ƴan uwan amaryarsa sannu ga shi sai hidima yake masu kamar dai zai goyasu dan so,haka kawai gaban Fandi ke ta faɗuwa,sanda ta samu wata babbar yayarsu Yagana ta faɗa mata ƴan kawo amarya suna hanya,dama kuma sune suke ta hidimarsu da sauran ƴan gidansu,yaranta kuwa suna can suna ta wasansu ba hankali ne da su ba bare su gane me ake ciki,nan tai shigewarta ɗaki ta kwanta saboda wani irin ciwon da kanta ke yi,bayan sallar asr motoci daga garin Sokoto suka fara parking ƙofar gidan,guɗa da shewar mata ya tabbatarwa ƴan uwan Fandi amarya da danginta sun iso...This book isn't for free,normal ₦300 posting 5 days excluding weekend,VIP ₦500 posting daily,SP 1K all via 0060746882-Hauwa Muhammad Usman,access bank. Then u show ur evidence of payment via https://wa.me/+2348165726609. If u are willing to pay,my sister pay it now before the price will go up,after it is completed the price is ₦500.
#Follow
#Vote
#Comment
#Share fisabilillah!
#Asli Smasher.
YOU ARE READING
CIWO A JIKIN WANI!
Romance...Shin me yasa mahaifi zai mayar da ƴaƴansa tamkar hannun jarin da zai tsammaci samun riba a ko da yaushe? '''ƊANƊANO..''' •••Hawaye sosai suke saukowa idonta da wani irin Baby voice tace "ban yi sallama da su Yaa Aalima ba" Hamdiyya dake ku...