Part 1

739 27 3
                                    

*GUDUNA AKEYI*

*NA*

_MUNEERA_

*DUKAN YABO DA GODIYA SUN TABBATA GA ALLAH MADAUKAKIN SARKI ME KOWA ME KOMAI DA YA KARA BANI DAMAR KAWO MUKU SABON LITTAFINA ME SUNA A SAMA DAFATAN ZAKU BANI HADIN KAI MASOYA NAGODE*

*WANAN LABARIN KIRKIRAREN LABARI NE DA NA KIRKIRO SHI DAKAINA IN KAJI/KINJI YAYI DAI DAI DA RAYUWAR KU TOH AKASI AKA SAMU*

"DAN ALLAH INA NEMAN ALFARMAR DUK WANDA YAGA NAYI BA DAI DAI BA KAR YAJI KOMAI YA MIN GYRA ZAN KARBA KO DAGA WURIN WAYE NAGODE*

*NIDIN BA MA'ABOCIYAR YIN TYPING ME YAWA BACE DAN ALLAH KAR AMIN KORAFIN TYPING KU BINI A HANKALI HAR NA AJIYE AL_QALAMINA NAGODE*

GA MASU SON ANTAYAWA GRP DIN MU GA LINK NAN 👇
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KN3yt830U4w4OTmxrTajKe


Dan Allah Don annabi in kinsan bazakiyi comment ba Karki shigo 🙏🏽🙄 masu comment kuwa Muna muku maraba da zuwa thank you 🥰🙏🏽❤️

*BISMILLAHI RAHMANIN RAHIM*

*1/1/2022*

*katsina state*

*qauyen danja*

Lulumin Sanyi la'asar ne ke busa ko ina yayin da kowani Dan Adam kokari yake yaga ya koma gida saboda sanyin da akeyi.

A hankali take tafiya kamar bazata taka kasa ba ko Kuma tsoron kasar takeyi a haka har ta karaso kofar gidan nasu wanda yake gidan 'kasa ne.

Gugun yan Daban dake kofar gidansu yasa ta sunkuyar da kanta' kasa.

Dan a duniya in akwai wadan da ta tsana toh yabi Bayan yan Daban nan na mahaifin ta.

Babanta na zaune a benchi wasu Kuma na gefen sa da gorori da Ada wasu Kuma suna wasa da karnukan su yayinda shi mahaifin nata Yana zaune Yana nad'a wiwin sa.

Har takai soron gidan Taji yace *ILHAM* gaban ta ya fadi cike da firgici ta juyo tare da dawowa wurin da yake.

Tace "barka da yamma Baba" ta fada gaban ta na faduwa saboda yanayin yarda ya ambaci sunan nata.

Cewa yayi " ke Dan uwar ki da kina ganin mutane Zaki wuce eyeeee shegiya me kama da aljanu"
Hawaye ya fara sintiri a Saman kumatun ta, "ba zakiyi magana ba ne senaci ubanki" ya fada muryarsa a karsashe cike da masifa.

A hankali ta furta "kayi hakuri Baba" batare da ya kale ta ba Taji Yana fadin "naji na hakura yar Baba" ya furta Yana busa hayakin wiwi Sama tare da fadin "tashi ki shiga ciki ki turo min 'kanin ki" cike da Jin dadin yarda baban nata ya hakura tace "toh Baba" Yana"kara busa hayakin Sama yace "jeki Allah yayi ALBARKA" Ta amsa da amin tare da mikewa tayi cikin gidan nasu.

Wanda a kauyen su din gidan su duk da na 'Kasa ne Amma yanada kyau tsarin ginin gidan irin gidan nan Dai na mutanen kauye fankacecen tsakar gida ne wanda babu simiti a KASAN.

Se dakuna kusan guda biyar, daya na mahaifin ILHAM, yayin da daya na ilham din ne, Se daya mahaifiya ilham din ne, Se dayan na kanene ilham ne dake duka maza ne, Se guda daga Chan farkon shigowa gidan shine na yaran mahaifin ilham wato yan Daban sa,

Gidan dan tsaf dashi Dan zaka iya jefar da lomar tuwo a tsakar gidansu ka dauke abun ka, ka cinye, maman ta na gefen murhu tana aza wuta Dan kamala uban abincin su da take yi wanda ba iya Ita kadai da yaranta take girkawa abincin ba harda yaran Daban baban ta.

Kowani daki dauke yake da kofar irin ta langalanga din Nan da Kuma labile a kowace kofa, da widows din dakuna gefe guda Kuma katon kitchen ne da yan Kaya yanki su na abinci a ciciki, Se gefe guda katon bandaki (toilet) wanda yayi daki guda Shima da rufinsa tabbas gidan ko a kauyen babba ne, (babanta ya Shahara a daba Dan sun iya kwacen Dabobi, babur, Keke da sauran su yaran sa har kudi yake biya musu su shiga birni suyi kwacen waya Kuma gaba daya yan Daban nan da Dakin su guda a cikin gidan shi yake ciyar dasu har da wadan da yake biyawa kudin makaranta shiyasa ko me gari tsoron sa yake ji domin Yaron yan siyasa ne ko kamashi akayi a ranar ake sakin sa saboda yarda yasan mutane)

Se yanzu na Kare Mata kallo mana Kallon ta zaka hango tsananin kamar ta da larabawa irin larabawa Somalia din Nan yarinya ce da bazata wuce 16yrs ba tana da tsahi wanda ba Chan sosai ba, sedai baxaka Kira ta da gajera ba sanan tana da diri sedai Kuma siririya ce, Amma Allah ya Bata diri dan wasu su kanyi zaton ta haura shekarunta sedai kana Kallon ta zaka gane yarinya ce,
fara ce Amma ba Chan sosai ba tana da ido Amma yanayin sa irin na masu Jin bacci ne (sleeping eyes), Se hancin ta wanda yake siriri ne kamar biro Bakin ta kuwa pink ne Dan sekayi tsamanin jambaki tasaka, Allah ya Mata baiwar gashi Dan gashin ta kuwa ya sauka har gadon bayanta, yarinyan Dai Allah ya Mata kyau duk wanda ya kaleta Sau daya Se ya Kara Kallon ta saboda kyaunta, kana Kallon ta zaka gane sanyin halinta da Bata cika magana ba murmushi shine magi yawancin maganar ta Bata da hayaniya ko ta kadan, (ILHAM yarinya ce me hakuri, , sanyin hali, kau da Kai, tausayi da Kuma juriya
duk kauyen su bame kyaunta a halin da ake ciki duk sa'a in ta sunyi aure itace Dai saboda tsoron mahaifin ta yasa batayi aure ba kowa tsoron sa yake ji saboda baya barin ta kwana Akan ILHAM duk wani Abu na yan birni shi yake Mata duk talaucin sa Yana fitar da kudi ya siya Mata sutura masu kyau amata dinki masu kyau a birni waya babba ya siya Mata a cewar sa bazata auri Dan kauye ba Dan birni zata aura ta wuce ajin yan kauye sedai birni shiyasa kowa yake tsoron kula ta)

A hankali cikin sanyi ta karasa wurin mahaifiyar Tata wace kana Kallon ta zaka gane mahaifiya ta ce.

Sedai basa kama Sam ita mahaifiyar kana Kallon ta zaka gane bafula tana ce wace bazata wuce shekaru Talatin da biyar ba a duniya bawata babba bace sedai yanayin rayuwa da zesa kayi Mata Kallon yar shekara ARBA'IN.

Tafi mahaifiya Tata kyau sedai mahaifiya tata ta nuna Mata haske Dan itama ba lefi tanada kyau sedai wahalar da take sha ne ya boye asalin Kyauta.

"Mama sannu da aiki" ta fada tana ajiye jakar islamiyya din ta.
Ba tare da ta kale ta ba tace yauwa *ilham* andawo kenan, "eh mama yau Dai Allah yasa munyi sauka" ta karashe maganar tare da nufo inda maman take.

masha Allahu maman ta Bata amsa "yaushe za'ayi taron yaye ku?" ta fada cike da zakuwar Jin me yarinya Tata zata ce, "mama ai Wai su ba'a bikin yaye dalibai a makarantar sun ce bidi'a ne ",se a lokacin maman ta kale ta sanan ta furta " toh Allah yasa ta tsoron Allah ce," ta amsa Mata da Amin suka cigaba da girkin tare sunayi suna Dan hira abun su sama² gwanin sha'awa

A buge mahaifin nasu ya shigo nan fa idon sa ya kyalo ilham a gaban murhu.

Wani uban ashar ya dura tare da fadin wani Dan shegiyar ne yasa ta aiki a gaban murhu, cikin sanyi irin na ilham jikinta ya fara rawa, gaban ta ya fadi hankalin ta ya tashi saboda tasan ba ita ze wa fada ba mahaifiya ta zeyiwa

"bawanda yasani ni nasaka kaina" ta fada tana hadiye wani mugun miyau me daci, tare da murza hanun ta,

tangadi ya fara yana taku irin na makaku tafiya Yana nufar inda mahaifiyar Tata take ze cakomo ta ya Mata duka yarda ya saba
ilham Tai saurin tare mahaifiya Tata ta fara kwala tare da fadin Baba bawanda ya saka ni fa Nina saka kaina cikin maye yace" no no impossible a Wahalar min dake nida nake so ki auri Dan birni haddade za'a dinga saki aiki fatarki ta lalace a banza"
ilham hawaye ya zubo Mata tace ya hakuri baban ilham, muje na raka ka daki, ta fada tana me jan hanunsa yayi kwafa tare da nuna mahaifiyar ilham da yatsa Yana fadin ki kiyaye ni Akan yarinyan nan atoh, ilham taja hanun mahaifin nata dake tangadi Yana nuna mahaifiyar ilham da yatsa Yana maganganun sa.

ilham Kuma najansa har daki ta kwantar dashi tana me Kallon mahaifinata tare da fadin"baba" cikin maye ya amsa ta fashe da kuka duk da a maye yake Amma kukan nata ya daga masa hankali yace yar Baba menene cikin sanyi da yanayin ta na rashin son yin magana tace "Baba wanan shashayen ne banaso naga kana yin sa" duk da a maye yake Se ya tsaya.

"yar Baba zan Dena kinji ai tunda bakyaso ma shiyasa na rage na Dena saboda a rayuwa ina matukar son ki ilham ina kaunar ki Bana kaunar abunda ze 'Bata Miki rai kinji ina kokari naga nadena Amma a hankali gashi na fara ragewa ko?"

Ilham ta girgiza cike da quncin zuciya na halin mahaifinata tace toh Baba yace yauwa Allah ya Miki albarka ya kawo miji Dan birni ita Dai abun na Bata mamaki wato Bama miji nagari ba shidai kawai ta auri Dan birni Allah ya shirya Mata mahaifinata

*TOH FANS GANI NAN NA DAWO DA FATAN ZAKUYI MIN COMMENT DA VOTE KAI HARMA DA SHARING ❤️😘 SABODA TSAKANINA DAKU ONE LOVE NE INA MATUKAR KAUNAR DUK WANI ME KAUNA TA*

GUDUNA AKEYI Where stories live. Discover now