DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN QAI.!
KAAMILAH!
01.
ƘAUYEN KARMAMI.
1998.
FARKO.
"Juma".
Ammi ta faɗi tana kama haɓa, gami da nuna alamun mamaki ta hanya fiddo da idanunta waje sosai, masu kama da ƙwan tsaka. Kafin ta lumshesu a hankali. Zuciyarta taji tana kara tunzura ta, akan ta amince da zancen da Juma ta zo mata dashi wanda ta tabbatar in tayi amfani da shawarar ba ƙaramar biyan buƙata za ta samu ba.
Sai dai kuma in tayi wani tunanin ta taɓa wannan kudirin amma kuma haƙarta ba ta cimma ruwa ba don ta tabbata Maqsood ya ji labarin za ta sake tura Zubaida yawon bara tabbas ba za su kwashe ta dadi dashi ba.
'Ɗan ki ne fa ke kika haifeshi a cikin ki. Dole ya bi abin da kika ce dashi in har yana neman albarkarki".
Wani sashi na zuciyarta ya shiga zayyona mata. A hankali ta tura laɓenta na ƙasa cikin baki ta ciza tana mai sake duban Juma wacce tayi ƙasake tana faman gabzar goro bakin nan nata yayi ciɗin-ciɗin da tukar goro laɓɓan sun yi jajir ko yaya ta buɗe bakinta kana hango jajayen haƙoranta da suka fice daga hayyacin su.
"Ba ke za ki wahala ba. Sannan ba jari za ki zuba ba bare ki ce kina tsoron asara. Riba ce kawai ta zallar kuɗi za ta ke kawo miki kina zaune a ɗaki".
Ɓarin zuciyarta ta sake zayyana mata cike da ƙarfafa mata guiwar ta amince da shawarar Juma da kuma na zuciyarta ta.Sai dai duk da Maqsood ɗan tane tana jin shakka akansa musamman in akace al'amari ya ta'allaƙa da Zubaida ne rayukar kowa ɓaci yake a gidan. Sai dai kuma a wannan karon ba ta jin akwai wani rai mai motsi da zai hanata cimma burinta game da Zubaida. Dole ta bi umarni da zata ginya mata in har ta buƙatar rayuwa cikin aminci a gidan nan. Ubanta dake iko da ita ya shuri burji. Maqsood shi kuma yana wajan yawon gantalin karatun bokon da ya ƙwallafawa rai wanda bata da tabbacin dawowarsa nan kusa.
"Ammi ki kula da Zubaida. Rauninta yana da yawa don Allah kar ki takura mata akan abin da kika san ba za ta iya shi ba. Na miki alƙawari ko na tafi zan dinga yi miki aike zan kama sana'a acan in na samu faragar karatu. Ban da talla Ammi kar Zubaida tayi talla ki bar ta a iya makaranta kawai. Ko aike in me nisa kar ki tura ta ki samu yaro ko nan maƙota ne ba za su ƙi zuwa ba. Don Allah Ammi ki min wannan alƙawarin".
Kalamansa ne suka shiga dawo mata a ranar da zai bar ƙauyensu zuwa birni don cigaba da karatunsa na boko. Karatun da tace ita bata ga amfaninsa ba illa ɓata lokaci. Amma ya nuna mata cewa ƙaratu shine ginshiƙin rayuwar duk wani matashi mace ko namiji sannan yana so ya yi karatu ne don tallafar rayuwar Zubaida da lalurarta.
Sai dai a yanzu bata jin wannan alƙawarin na Maqsood zai yi amfani don tuni ta sanya ƙafa ta shure shi gami da murjewa kamar yadda shi ma ya shure alƙawarin zai dinga yo mata aiƙe gashi yanzu kusan watansa biyar kenan da tafiya zuwansa biyu amma me ya haɗa dashi illa dubu uku kacal suma kafin ya tafi dashi aka lashe su a girkin gida.
Don haka ba ta jin zata tsaya jiran tsammanin warabbuka. Bata jin zata tsaya ta shure hanyar samu da ta zo mata a saukaƙe ta ɗauki hanyar da bata da tabbas ina! Hakan ma ba zai yuwu ba.
YOU ARE READING
Kaamilah!
Non-FictionDa za ace mata in ta shigo duniya za ta tadda kalar rayuwarta da ƙwarin guiwa zata ƙarya ta ko waye. Sai dai kuma ƙwarin guiwa da ƙarfin zuciya da take dashi tuni su bi iska ba tare da ta yi tsammanin hakan ba. A lokacin da ta ɗauki yarda da...